ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, November 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Bala Ne Ya Jefa Al’ummar Bauchi Cikin Matsin Rayuwa Ba Tinubu Ba – Sanata Shehu Buba

by Sulaiman and Khalid Idris Doya
1 year ago
Gwamna Bala

Sanata Mai Wakiltar Mazabar Bauchi ta Kudu, Sanata Shehu Buba Umar, ya ce, suka da caccakar da gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad ya yi wa shugaban kasa Bola Tinubu kan matsin rayuwa da ake ciki, ya yi ne kawai domin karkatar da hankulan jama’an jihar daga maƙudan biliyoyin nairori da tulin tirelolin kayan abinci da gwamnatin tarayya ta turo jihar.

Ya kuma ce, gwamnatin jihar ta PDP ce ta kakaba wa jama’an jihar yunwa da matsin rayuwa domin gwamnatin tarayya ta bayar da tirelolin shinkafa, taki, dawa domin rabar wa jama’a kyauta, ya zargi gwamnatin jihar da cewa ba ta rabar ba.

ADVERTISEMENT
  • Ba Mu Samu Umarnin Ƙara Alawus Ɗin Masu Hidimar Ƙasa Ba – NYSC
  • Rashin Sani Ne Ya Sa Wasu Ke Karyata Ikirarin Da Na Yi Na Samun Kyautar Motoci 75 -Mai Dawayya

Sanatan ya yi wannan ikirarin ne a yayin da ya ke jawabi a ƙarshen mako yayin bikin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓe da miƙa wa ‘yan takara tuta na zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi 20 da kansiloli 323 da zai gudana a jihar Bauchi ranar Asabar 17 ga watan Agusta.

LABARAI MASU NASABA

Da Ɗumi-ɗumi: PDP Ta Kori Wike, Fayose, Anyanwu Da Wasu Mutane 7

Sanusi II Kaɗai Muka Sani A Matsayin Halataccen Sarkin Kano – Kwankwaso

Buba ya ce: “Talaucin da ake ta kuka a jihar Bauchi, gwamnatin jihar ce ta assasa mana shi. Bari na gaya mana, ni sanata ne da ke wakiltar Bauchi ta Kudu, duk abon da ake damawa a Abuja a idona ake yi. Ina gaya muku daga 2023 zuwa Janairu, jihar Bauchi ta karɓi fiye da naira biliyan 144 daga asusun hadaka na tarayya (FAAC), ina waɗannan kuɗaɗen suke? ya fito ya karyata abin da na fada.

“Daga watan 1 zuwa yau, jihar Bauchi ta karɓi fiye da naira biliyan 47, kuma zuwa ƙarshen shekarar nan za ta karɓi kuɗi kimanin naira biliyan 195. Amma yaushe zai zo ya tsaya ya yi ƙarya, ya ce wai gwamnatin APC ta kawo yunwa, balle kai ne kake riƙe da lalitar jihar Bauchi me kake yi wajen kawo sauyi a cikin tsanani da ake ciki?.

Gwamna Bala

“Al’ummar Bauchi su na kallonka kowa yana kallonka. Ina tabbatar muku cewa, yanzu kamar wata shida da suka wuce akwai tirololi na Dawa 70 da aka bayar a kawo wa jihar Bauchi, jihar Bauchi an ba ku? ina ya kai su?. ku tamabaye shi.

“Akwai Taki Tireloli 70 da aka bayar a kawo Bauchi kyauta amma yanzu ya zo yana sayar muku a kan naira dubu 50,000. Kwanan nan an bayar da tirelolin Shinkafa 20 don a kawo wa ‘yan jihar Bauchi, ya ba ku?

“To, waye ya riƙe kuɗaɗen da kayan abinci da ake kawowa daga gwamantin tarayya?

“Kuma kowa ya sani ya je ya ciwo bashi na sama da naira biliyan 300 kuma harƙar hanya ko kwangilar haya shi ya kawo kamfaninsa ne.”

Ya ƙara da cewa, “Mu muna zaman lafiya da kai ba mu nemeka da faɗa ba, kai ka tsokano mu ka zage ka, shi ya sa na ce yau za mu biyaka bashi guda ɗaya. Za mu saurareka mu ji amsarka, muna da dozin da za mu amayar wa mutanen jihar Bauchi.”

Gwamna Bala

Shehu Buba da yake magana kan zaɓen, ya tabbatar wa jama’a cewa a shirye APC take, har ma ya bada tabbacin cewa su ne za su lashe zaɓen shugabannin da na kansiloli muddin aka yi adalci.

Shi ma a nasa ɓangaren, shugaban jam’iyyar APC a jihar Bauchi, Muhammad Hassan Tilde, ya gargaɗi hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Bauchi kan yin maguɗi ko taimaka wa PDP da gwamnatin jihar su yi musu maguɗi, ya ce, a shirye suke su kara da kowace jam’iyya kuma su yi nasara.

Ya nemi wakilansu da masu sanya ido da su gudanar da ayyukansu yadda ya dace domin daƙile abun da ya kira shirin musu maguɗi.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Da Ɗumi-ɗumi: PDP Ta Kori Wike, Fayose, Anyanwu Da Wasu Mutane 7
Da ɗumi-ɗuminsa

Da Ɗumi-ɗumi: PDP Ta Kori Wike, Fayose, Anyanwu Da Wasu Mutane 7

November 15, 2025
Yanzu Satar Da Kuka Yi Ba Ta Da Amfani: Kwankwaso Ga Gwamnonin APC
Manyan Labarai

Sanusi II Kaɗai Muka Sani A Matsayin Halataccen Sarkin Kano – Kwankwaso

November 15, 2025
NAF Ta Ragargaza Mafakar Ƴan Ta’adda A Zamfara, Ta Halaka Da Dama
Manyan Labarai

NAF Ta Ragargaza Mafakar Ƴan Ta’adda A Zamfara, Ta Halaka Da Dama

November 15, 2025
Next Post
Kungiyar Kasar Sin Ta Lashe Lambar Zinare A Gasar Kwallon Tebur Ta Kungiyoyin Mata A Gasar Olympics Ta Paris

Kungiyar Kasar Sin Ta Lashe Lambar Zinare A Gasar Kwallon Tebur Ta Kungiyoyin Mata A Gasar Olympics Ta Paris

LABARAI MASU NASABA

Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN Sun Shaida Adawar Sassan Kasa da Kasa Da Burin Masu Tsattsauran Ra’ayi Na Japan Na Ruguza Odar Kasa Da Kasa Ta Bayan Yakin Duniya Na 2 Dangane Da Batun Taiwan

Hukumar Kwallon Kafa Ta Kasar Turkiyya Ta Dakatar Da ‘Yan Wasa 1024 Saboda Laifin Caca

Hukumar Kwallon Kafa Ta Kasar Turkiyya Ta Dakatar Da ‘Yan Wasa 1024 Saboda Laifin Caca

November 15, 2025
Sin Ta Bayyana Damuwa Dangane Da Matakin Amurka Na Ingiza Daftarin Tsawaita Aikin Tawagar UNISFA 

Sin Ta Bayyana Damuwa Dangane Da Matakin Amurka Na Ingiza Daftarin Tsawaita Aikin Tawagar UNISFA 

November 15, 2025
Za A Yi Gwanjon Rigunan Messi Na Gasar Kofin Duniya Ta 2022 Da Kudi Tsagwagwa

Ina Son Kasancewa Cikin Koshin Lafiya Kafin Buga Gasar Kofin Duniya Na Shekarar 2026 – Messi

November 15, 2025
Za A Wallafa Makalar Xi Game Da Gina Sabbin Ginshikan Samar Da Ci Gaban Kasa Masu Inganci

Za A Wallafa Makalar Xi Game Da Gina Sabbin Ginshikan Samar Da Ci Gaban Kasa Masu Inganci

November 15, 2025
Duk Niyyar Da Mutum Ya Shigo Da Ita Kannywood Ita Za Ta Bi Shi —HAUWA KUJAMA

Duk Niyyar Da Mutum Ya Shigo Da Ita Kannywood Ita Za Ta Bi Shi —HAUWA KUJAMA

November 15, 2025
Sin Ta Sha Alwashin Bunkasa Goyon Bayan Juna Tsakaninta Da Saliyo

Sin Ta Sha Alwashin Bunkasa Goyon Bayan Juna Tsakaninta Da Saliyo

November 15, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: PDP Ta Kori Wike, Fayose, Anyanwu Da Wasu Mutane 7

Da Ɗumi-ɗumi: PDP Ta Kori Wike, Fayose, Anyanwu Da Wasu Mutane 7

November 15, 2025
An Gabatar Da Sabuwar Hanyar Raya Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Cinikayya A Tsakanin Sin Da Afirka

An Gabatar Da Sabuwar Hanyar Raya Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Cinikayya A Tsakanin Sin Da Afirka

November 15, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Yi Taka-tsantsan Da Batun Yankin Taiwan 

Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Yi Taka-tsantsan Da Batun Yankin Taiwan 

November 15, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.