Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya gabatar wa zauren majalisar dokokin Jihar Yobe kudurin kasafin kudin 2023 na kimanin N163,155,366,000, domin amincewa.
Da yake gabatar da kasafin kudin wannan shekara a ranar Alhamis, wanda aka yi wa taken: “Kasafin kudi domin ci gaba daga inda aka tsaya, karfafawa tare da sauya fasalin tattalin arziki” ga zauren majalisar dokokin jihar, Gwamna Buni, ya ce an yi kiyasin kasafin ne domin karfafa nasarorin da ya samu a baya wajen ciyar da jihar gaba.
- El-rufai Ya Amince Da Nadin Wazirin Garin Jere A Matsayin Sabon Sarkin Masarautar Jere
- Babban Joji Ga Alkalai: Kar Ku Ci Amanar ‘Yan Nijeriya A 2023
Kasafin kudin 2023 ya ragu da kashi 0.49 cikin 100, idan aka kwatanta da na shekarar 2022 da ta gabata.
Yayin da a cikin kasafin aka ware N87,800,717,000 wajen gudanar da ayyukan gwamnati na yau da kullum, kimanin kaso 57 cikin 100 na adadin kasafin kudin.
Bugu da kari kuma Gwamna Buni, ya bayyana cewa, an ware jimillar N75,354,649,00 a bangaren manyan ayyukan da gwamnatin jihar za ta aiwatar a wannan shekarar, wanda ya tsaya madadin kaso 43 cikin 100 na kasafin kudin.
Ya kara da cewa kasafin kudin zai karkata ne wajen kammala ayyukan da ake ci gaba da aiwatarwa domin cimma muradun gwamnati wajen farfado da yankunan da rikicin Boko Haram ya tagayyara a jihar, bunkasa harkokin ci gaba da inganta tattalin arziki da walwalar jama’ar jihar.
Ya ce gwamnati za ta ci gaba da kokarin da ta ke wajen gina tituna, da farfado da fannin ilimi da kuma kudirin kammala sauran cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko, a karkashin kudurin gwamnatin jihar na kafa cibiyar kiwon lafiya a matakin farko guda daya a cikin kowace gunduma daga cikin gundumomi 178 a fadin Jihar Yobe.
A nashi bangare, kakakin Majalisar Dokokin Jihar Yobe, Ahmed Mirwa, ya bayar da tabbacin aiki tukuru wajen ganin zauren majalisar ya duba kasafin kudin tare da amincewa da shi domin bai wa bangaren zartaswa damar gudanarwa da al’ummar Jihar Yobe ayyukan ci gaba, wadanda suke kunshe a cikin kasafin kudin na 2023.