Gwamnan jihar Adamawa Rt Hon Ahmadu Umaru Fintiri, ya maka dakataccen kwamishinan hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa reshen jihar, Barista Hudu Yunusa Ari l, a gaban babbar kotun jihar bisa zargin aikata laifuka lokacin gudanar da babban zaben 2023.
Gwamnatin jihar dai, na neman kotun da ta yanke hukunci kan sabbin tuhume-tuhume 3, da laifukan da take zargin Hudu Ari da aikatawa a lokacin da yake tafiyar da harkokin hukumar zabe INEC a jihar.
- Za Mu Tabbatar Kotu Ta Hukunta Dakataccen Kwamishinan Zaben Adamawa Hudu Ari – Fintiri
- Jam’iyyun Hamayya Ku Zo Mu Haɗa Kai, Mu Gina Jihar Adamawa – Fintiri
Haka kuma baya ga tuhumomin uku, da gwamnatin ta shigar gaban mai shari’a Benjamin Manji Lawan, akwai kuma batun yunkurin hargitsa zaman lafiyar jama’ar jihar da aikata laifukan da ka iya haifar da rashin zaman lafiya da kuma yin aiki da wani jami’in gwamnati.
Wannan ya kaiga tuhume-tuhume kusan 9 a cikin kararraki 2 daban-daban da gwamnatin tarayya ta shigar da Hudu Ari, da kuma gwamnatin jihar Adamawa da ke neman kotu ta yi masa shari’a tare da hukunta shi kan laifukan.
Gwamnatin tarayya ta yi fatali da tuhume-tuhume 6 da ake tuhumar Hudu Ari, to sai dai shari’ar ta kasa ci gaba, saboda gaza gurfanar da shi a gaban kotu, an kuma dage shari’ar kusan 9.
A sabbin tuhume-tuhumen da gwamnatin jihar ta shigar mai alamar: HC/ADSY/9c/2024, an shigar da karar ne ranar 20 ga watan Fabrairu 2024.
Da yake jawabi a kotun, Lauyan gwamnatin jihar, Akamode Abayomi, ya shaida wa kotun cewa har yanzu ba’a gurfanar da wanda ake tuhuma ba, ya na mai cewa kokarin da aka yi na gurfanarwar bai yi nasara ba.
Mista Akamode, ya ce wa kotun wanda ake kara ba shi a adireshin jihar Bauchi kamar yadda aka ba su, ya ce an dade ba a ga gidan wanda ake karar ba.