Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da shirin ciyar da ɗalibai a makarantu a matakin gwaji, domin yaƙi da yunwa tsakanin yara, ƙarfafa zuwan yara makaranta da rage yawan yara marasa zuwa makaranta a faɗin jihar.
Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da shirin, Gwamna Lawal ya ce wannan shiri ba wai kawai na ciyar da yara ba ne kaɗai, zai bunƙasa ilimi da yaƙi da yunwa.
- Matawalle: Kofarmu Abude Take Idan Gwamna Dauda Lawal Na San Shigowa Jamiyyar APC
- Babu Wanda Ya Buƙaci Atiku Ka Da Ya Yi Takara A 2027 – ADC
Shirin ya na ƙarƙashin jagorancin Mai Baiwa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Ciyar da Ɗalibai a Makarantu (OSSAP-SF), Dr. Yetunde Adeniji, domin tallafawa yara marasa galihu a Nijeriya.
“Muna alfahari da aiki tare da shugabanni masu hangen nesa kamar Dr. Yetunde Adeniji domin cika alkawarin da muka ɗauka tare,” Cewar Gwamna Lawal.
Shirin yana samun goyon bayan manyan abokan hulɗa kamar Bankin Duniya (AGILE) da UNICEF da Cibiyar Ci Gaban Tattalin Arziki ta Duniya (ICED), da kuma FINPACT.
A nata bangaren, Mrs. Adeniji ta bayyana cewa akwai yawaitar yara marasa zuwa makaranta a ƙananan hukumomi 14 na jihar, tare da tabbatar da cewa ta hanyar wannan shirin zai taimakawa ɓangaren ilimi a jihar Zamfara.
“Muna aiki tare domin tabbatar da cewa babu wani yaro da aka bari s baya,” Cewar ta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp