Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na kafa ƙa’idojin gudanar da nagartattun ayyukan gwamnati a cikin ma’aikatun gwamnatin jihar.
A ranar Alhamis ne gwamnan ya ƙaddamar da wasu kwamitoci shida domin aiwatar da sauye-sauye da tsare-tsaren samar da sabuwar jihar Zamfara, a tsohon ɗakin taro na gidan gwamnati da ke Gusau.
- Gwamnatin Tarayya Ta Sha Alwashin Kawo Karshen Ayyukan ‘Yan Ta’adda A Arewa Maso Yamma
- MOFA: Ministan Harkokin Wajen Birtaniya Zai Ziyarci Kasar Sin
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa kwamitocin da aka ƙaddamar sun haɗa da Kwamitin Inganta Rayuwar Bil’adama, Kwamitin Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi, Kwamitin Amfani da Filaye da Rabon Filaye, da kuma Kwamitin Tsare-tsare na Raya Ƙasa.
Sanarwar ta ƙara da cewa, sauran kwamitocin da aka ƙaddamar sun haɗa da Kwamitin Samar da Hanyoyin Inganta Rayuwar Al’umma da kuma Kwamitin Bankin Duniya na Magance Matsalar Matsugunai a yankuna.
A wajen ƙaddamarwar, Gwamna Lawal ya sake nanata cewa an aiwatar da hakan ne a tsakani inda aka zaƙulo waɗanda za su yi wannan gagarumin aiki da suka haɗa da Majalisar Zartarwa ta Jihar, Manyan Sakatarori, masu fasaha, malamai, jiga-jigan gudanarwa, da ɗaiɗaikun mutane.
“Kwamitin Inganta Rayuwar Bil’adama zai kasance ƙarƙashin Mataimakin Gwamna, Mani Mallam Mummini Masarar Mudi, tare da Babban Mai Taimakawa na Musamman a kan Cigaban Al’umma a matsayin Sakatare.
“Aikin wannan kwamiti shi ne tabbatar da ingantaccen tsarin tafiyar da al’umma wanda zai inganta ɗorewar ayyukan gwamnati da shirye-shiryen ci gaban bil’adama. Har ila yau, zai daidaita ayyukan ma’aikatu masu alaƙa da bunƙasa ci gaban al’umma da kuma kawar da cikas a cikin ayyuka da dama.
“Ta hanyar wannan kwamiti, gwamnati za ta tabbatar da ingantaccen ilimin da jama’armu suka samu, musamman matasa da mata, don ba su damar amfani da ilimin wajen ci gaban al’umma.
“Kwamitin na biyu yana da alhakin magance matsalar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi a jihar. Wannan kwamiti zai gudanar da cikakken aiki a kan daƙile shaye-shayen miyagun ƙwayoyi a cikin al’ummominmu, tare da yin nazarin nau’ikan magungunan da ake amfani da su, da ƙididdigar masu amfani da su, da kuma yawan yaɗuwarsa.
“Bugu da ƙari, zai binciki tushen abubuwan da ke haifar da shaye-shayen ƙwayoyi tare da ba da shawarar dabarun riga-kafi da shiga tsakani. Uwargidan gwamna, Hajiya Huriyya Dauda Lawal ce za ta shugabanci wannan kwamiti, sannan sakatariyarta za ta kasance daraktar ma’ajin magani na Ma’aikatar Lafiya.
“Kwamitin na gaba shi ne wanda zai tabbatar da kammala shirin raya jihar Zamfara na shekaru goma, 2024-2033. Aikin sa shi ne tabbatar da cewa an aiwatar shirin raya jihar wanda aka gabatar watanni biyu da suka gabata, da kuma tabbatar da cewa ya yi daidai da yadda aka tsara.
Wannan kwamiti kuma zai samar da hanyoyi cikin harkar gwamnati don cimma maƙasudin shirin. Zai kuma yi aiki kafaɗa da kafaɗa tare da ofishin Hukumar kula da yara ta Duniya UNICEF na yanki da ke Sakkwato domin tsare-tsare, aiwatarwa, amincewa da ƙaddamarwa. Kwamishinan ilimi, kimiyya da fasaha, Malam Wadatau Madawaki ne zai shugabanci wannan kwamitin.
“Kwamitin amfani da rabon filaye, shiri ne na dabarbaru, shi ne zai samar da tsarin tafiyar da harkar filaye. Shi ne tattara takardun neman filaye, ya ba Gwamna shawarar waɗanda suka cancanci a ba su filayen, wannan kwamiti ne dai kuma zai bayar da shawarar filayen da za a iya ƙwacewa idan ya yi karo da waɗansu buƙatu.
“Bugu da ƙari, wannan kwamiti ne kuma zai tantance biyan diyya ga wuraren da aiki ya bi ta kan su. Gogagge a harkar filaye da safiyo, kuma Tsohon Babban Sakatare, Alhaji Ali Boko ne zai jagoranci wannan kwamiti.
“Kwamitin kula da harkokin ‘yan gudun hijira, ‘yan ƙasa, wanda shiri ne na Bankin Duniya ne, Kwamishinan kasafi da tsare-tsare, Abdulmalik Abubakar Gajam ne zai shugabance shi. Wannan kwamiti ne ke da alhakin aiwatar da tsarin Bankin Duniya game da ‘yan gudun hijira da ayyukan ci gaban ƙasa, wanda ma’aikatar kasa da tsare-tsaren tattalin arziki ta tarayya ke jagoranta.
“An samar da wannan shiri ne don inganta rayuwar ‘yan gudun hijira da ‘yan ƙasa a yankunan Ƙananan Hukumomin da abin ya shafa a Arewacin Nijeriya, wanda jihar Zamfara na ciki.
“Kwamiti na ƙarshe da aka ƙaddamar shi ne Kwamitin samar da hanyoyin inganta rayuwar ɗan adam don ci gaba, da kuma daidaito a harkar gwamnati.
“Wannan wani bangare ne na shirin kasa da jihar Zamfara ke da niyyar gudanarwa.
Wannan shirin ya ƙunshi ayyuka guda uku masu dogaro da juna waɗanda aka tsara don magance ƙalubale daban-daban da tallafawa da kuma rarraba albarkatu da haɓaka kashe kuɗi don ilimin firamare da ayyukan kiwon lafiya a matakin farko.
Kwamitin zai mayar da hankali kan ƙara samar da inganci na samar da kuɗaɗe don ilimin firamare da kiwon lafiya, inganta gaskiya da riƙon amana, da inganta ɗaukar ma’aikata da gudanar da ayyukan malamai da ma’aikatan kiwon lafiya.”