• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Lawal Ya Jinjina Wa Obaseki Kan Shirin Inganta Kiwon Lafiya A Jihar Edo 

bySulaiman
11 months ago
Gwamna lawal

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yaba wa Gwamna Godwin Obaseki kan yadda ya kawo sauyi da kuma ƙudirinsa na inganta fannin kiwon lafiya a Jihar Edo.

Gwamnan ya kasance babban baƙo a wajen bikin ƙaddamarwa, rantsar da sababbin ɗalibai da kuma cika shekaru 60 da kafa Kwalejin Kimiyyar Kiwon Lafiya da Fasaha ta Edo (EdoCOHEST) da aka gudanar a birnin Benin a ranar Larabar da ta gabata.

  • Majalisar Dattawa Ta Amince Da Ministoci 7 Da Tinubu Ya Nada
  • ‘Yan Bindiga Ba Su Karɓe Sansanin Horo Da Ke Neja Ba – Hedikwatar Tsaro

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa bayan ƙaddamar da kwalejin, gwamnonin sun zagaya da kayayyakin zamani da aka samar a ginin.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

A lokacin da yake gabatar da jawabinsa, Gwamna Lawal ya ba da shawarar cewa jihohin biyu su kafa shirin musayar ɗalibai, wanda zai bai wa ɗalibai mata da ke makarantun kiwon lafiya a Zamfara damar zuwa kwalejin Edo domin yin wani zagon karatu.

Gwamna lawal

Ya ce, “Haƙiƙa babban abin alfahari ne da kuma gata kasancewata a nan wurin tare da ɗan uwana da mutanen kirki na jihar Edo don buɗe wani sabon babi na Kwalejin Kimiyyar Kiwon Lafiyar da Fasaha ta Edo, musamman ga ɗaliban da suka shigo yanzu.

“Yayin da muka taru a nan, ina jinjina irin hangen nesa da jajircewar ɗan uwana Gwamna Obaseki, wanda ya sake farfaɗo da fata a Jihar Edo cikin kyakkyawar manufa, za a iya samun ɗaukaka duk da rashin daidaito a ƙasarmu mai albarka.

“Lokacin da na samu bayanai game da wannan ingantaccen aikin gaba ɗaya, na yaba kuma na jinjina wa ɗan uwana kan irin wannan manufa da za a iya cimmawa kaɗai ta bangaren juriya, hangen nesa da sadaukarwa.

“Ga ɗaliban da suka shigo a yau, zan ce ku ne burinmu kuma alfaharinmu. Kuna wakiltar jihar Edo da ƙasar mu gaba ɗaya ne. Don haka kada ku iyakance kanka.

“Ku yi karatu kuma ku yi fice a karatun; ku daraja aikin da ɗan uwana ya yi a yau don kanku da ɗalibai a nan gaba.

Gwamna lawal

“Baya ga samar da ƙwararrun masana kiwon lafiya, ina addu’a cewa wannan kwaleji ta zama wata gada ta haɗa kan jama’a, samar da ayyukan yi, da bunƙasar tattalin arziki a ciki da wajen jihar Edo. ”

Gwamna Obaseki ya gode wa Gwamna Lawal bisa girmama gayyatar da mutanen jihar Edo suka yi masa.

“Ina matuƙar godiya da kai ɗan uwana Gwamnan Jihar Zamfara, Dokta Dauda Lawal da ka zo min wannan biki mai bangarori uku, wanda ya hada da ƙaddamarwa, rantsar da sabbin ɗalibai, da kuma cika shekaru 60 da kafa Kwalejin Kimiyyar Kiwon Lafiya da Fasaha ta Edo (EdoCOHEST).”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio
Manyan Labarai

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo
Manyan Labarai

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

October 7, 2025
Ya Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa
Manyan Labarai

Ya Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa

October 7, 2025
Next Post
Mun Kaɗu Matuƙa Kan Labarin Mutuwar ‘Yan Mauludi A Hanyar Saminaka – Gwamnan Kaduna

Gwamna Sani Ya Amince Da ₦72,000 Mafi Ƙarancin Albashi Ga Ma’aikatan Jihar Kaduna 

LABARAI MASU NASABA

…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Tinubu

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk 

October 7, 2025
Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version