A ƙoƙarin da ya ke yi don ganin ya cika alƙawuran da ya yi wa Zamfarawa, musamman a harkar ilimi, Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya samu nasarar karɓo sakamakon jarabawar WAEC na ‘yan asalin jihar, wanda Hukumar ta ƙi saki saboda rashin biyan kuɗin jarabawar.
Ita dai Hukumar da ke kula da shirya jarabawar ta WAEC ta riƙe sakamakon jarabawar ɗaliban jihar Zamfarar ne sakamakon bashin Naira Biliyan 1.4 da ta ke bin gwamnatocin jihar da suka gabata.
- Zannan Bungudu Ya Gina Masallatai 20 Makarantun Islamiyya 15 A Jihar Zamfara
- Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin ‘Pulaku’ Don Kawo Karshen Rikicin Manoma Da Makiyaya
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawu Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa Gwamnan ya samu ganawa da shugabannin Hukumar ne a ofishin sa da ke Abuja ranar Litinin da ta gabata.
Ya ce, a ziyarar da suka kawo wa Gwamnan, sun samu ganawa da shugabannin Hukumar bisa jagorancin shugabar sashen mulki da harkokin kuɗi, Hajiya Binta Abdulkadir da kuma shugaban ofishin WAEC, Dr. Amos J. Dangut.
Ya ci gaba cewa, “A ƙoƙarin da gwamnatin nan ke yi na ganin ta haƙƙaƙa shirin ta na sanya dokar ta-ɓaci a harkar ilimi, Gwamna Dauda Lawal ya karɓi baƙuncin Shugabannin Hukumar WAEC a ofishin sa da ke Abuja.
“Gwamnan, wanda ke tare da Kwamishinan ilimi, kimiyya da fasaha, Mallam Wadatau Madawaki, sun tattauna da shugabbanin Hukumar ta WAEC a kan abin da ya shafi basussukan da ake bin jihar Zamfara na gwamnatocin da suka gabata.
“Rashin biyan waɗannan kuɗaɗe na tsawon shekaru ya sa hukumar ta ƙi bayyana sakamakon jarabawar ɗaliban jihar suka zana, wanda wannan yanayi ya jawo wa ɗaliban da suka kammala Jami’o’i rashin zuwa yi wa ƙasa hidima na NYSC saboda rashin sakamakon na WAEC a hannun su.
Sanarwar ta Idris ta ƙara da bayyana cewa, a wancan zaman, an cimma matsaya tsakanin gwamnatin jihar Zamfara da Hukumar ta WAEC kan yadda za a shawo kan lamarin bashin.
“A ƙarshen zaman, Hukumar ta amince za ta fitar da sakamakon jarabawar da suka gabata, tare da amincewa ɗaliban jihar za su zauna don zana jarabawar WAEC ta shekarar 2024.
“Duk ɓangarorin byu sun amince da tsarin da aka yi na biyan bashin da ake bi, tare da cewa za a saki sakamakon jarabawar kafin ƙarshen watannan.”
A wannan ganawa dai, akwai manyan ma’aikatan Hukumar, waɗanda suka haɗa da Mr Ambrose Okelezo, shugaban shiyya; Mr Victor C. Odu, Daraktan kuɗi; da Mr Segun U. Jerumeh, Mataimakin Darakta.