A wani yunkuri na inganta harkar noma a jihar Zamfara, Gwamna Dauda Lawal ya jagoranci rabon muhimman kayan Noma a karkashin shirin (N-CARES).
Sakamakon illar da cutar sarkewar numfashi ta Covid-19 ta haifar, ta kawo naƙasu da koma baya a harkokin noma da kiwo a Nijeriya.
- Dangote Ya Sauko Daga Matsayin Attajirin Da Ya Fi Kudi A Afrika
- Majalisa Ta Amince Tinubu Ya Ciwo Bashin Naira Tiriliyan 7.5
Gwamna Lawal a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sulaiman Bala Idris ya rabawa manema labarai, ya bayyana hanyoyin da gwamnatin jihar za ta bi wajen bunkasa noma a jihar, ciki harda wannan tsarin (N-CARES) na tallafawa manoma.
An kaddamar da shirin ne da shiyyar arewacin jihar a ƙaramar hukumar Shinkafi tare da manoman yankin.
Manoman da suka ci gajiyar tallafin a shiyyar sun samu cikakken tsari wanda ya haɗa da bada iri, kayan noma har tsawon shekaru hudu.
Sanarwar ta bayyana kudirin gwamnatin jihar na magance fatara da habaka tattalin arzikin jihar Zamfara.
Gwamna Lawal da yake jawabi a wajen taron, ya jaddada kudirin wannan shirin in da ya ce:
“Gwamnatin jihar Zamfara ta fara yin hadaka wajen bunkasa noma ta hanyar samar da kayayyakin noma da kayayyakin more rayuwa da ake bukata a yankunan karkara,”
Kamar yadda yake a cikin sanarwa da mai magana da yawun gwamnan ya fitar, ta ce:
“Gwamnan ya kara da jaddada kudirin gwamnatinsa wajen yin aiki kafada da kafada da mazauna yankunan don inganta yanayin zamantakewa, musamman wajen amfani da shirin gwamnatin tarayya na FADAMA III”