• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Lawal Ya Rattaba Hannu Kan Kasafin Kudi Na Naira Biliyan 546 Na Shekarar 2025

bySulaiman and Hussein Yero
10 months ago
Gwamna lawal

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya rattaba hannu kan ƙudirin kasafin kuɗin shekarar 2025 na Naira 546,014,575,000.00.

Kasafin kuɗin 2025 mai taken; “Kasafin Ceto 2.0”, kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara ya gabatar wa gwamnan a ranar Alhamis a gidan gwamnatin jihar da ke Gusau.

  • Dakarun MNJTF Sun Daƙile Harin Da Aka Kai Sansanin Su, Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 10 A Kamaru
  • Dubun Sojan Gona Ta Cika Bayan Damfarar Mutane A Jihar Yobe

A yayin rattaba hannu kan ƙudirin kasafin kuɗi na shekarar 2025, Gwamna Lawal ya ƙuduri aniyar kammala dukkan ayyukan da ake gudanarwa tare da inganta nasarorin da aka samu a cikin watanni 18 da gwamnatinsa ta yi.

LABARAI MASU NASABA

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

Gwamnan ya bayyana muhimmancin kasafin kuɗin shekarar 2025, inda ya ce ‘ba wai kawai mu kalli inda muke ko kuma inda muka dosa ba, amma inda muka kasance’.

“Abin ya tsananta a bara. Shekaru goma na rashin shugabanci nagari ya haifar da durƙushewar tattalin arziki, rashin biyan ma’aikatan gwamnati albashi, da kuma basussukan da ke kawo cikas ga ilimin yara. An lalata ababen more rayuwa, an yi watsi da asibitoci, kuma ayyukan jama’a sun ɗaiɗaita. Bugu da qari kuma, akwai rashin bin doka da oda, da batun kuɗin wutar lantarki da ake ci gaba da yi, da rashin isasshen ruwan sha, rashin tsaro, da ƙaruwar cututtuka masu yaɗuwa kamar kwalara, tare da raguwar kuɗaɗen shiga na cikin gida.

“Da ba mu yi gaggawar magance dukkan ƙalubalen ba, da jihar Zamfara ba za ta zama wurin da dukkan mu za mu iya rayuwa a yau ba.

“Ƙudirin Ceto na 2025 2.0 yana gudana ne ta hanyar jajircewarmu na ci gaba da ayyukan da muka fara wa mutanenmu, wanda ke nuna kyawawan manufofi na kishi. Wannan kasafin kuɗin kuma ya sanya aka ƙara wa ma’aikata ƙarin albashi mafi ƙaranci, inda ya tashi daga N30,000 zuwa N70,000.

Gwamna Lawal ya bayyana cewa lokaci ya yi da jihar Zamfara za ta shawo kan lalacewar ababen more rayuwa da kuma ƙoƙarin inganta gine-gine.

Kasafin kuɗin 2025 zai shafi gudanar da ayyukan filin jirgin sama na Gusau da kuma aikin gina hanyar Gusau-Magami zuwa Dansadau.

“Hakazalika, Kasafin 2025 zai shafi samar da kayan aikin tsaro ta hanyar ‘Asusun Tsaro’, gina makarantu ta hanyar shirin Agile, kafa cibiyar bincike ta zamani, gina birnin na zamani, samar da abinci a ƙarƙashin shirin Fadama III, sauƙin kasuwanci ta hanyar ‘Saber Program’, gyara Cibiyar Bafarawa Shinkafi, da gina Cibiyar Taro ta Duniya.

“Aikin gina titin Lalan zuwa Lalan, inganta asibitin ƙwararru na Yariman Bakura zuwa asibitin koyarwa, gina ƙarin gine-gine a manyan asibitocin Anka, Kauran namoda, Gummi, Shinkafi, Magami, Tsafe, Jangebe, da Bukkuyum, inganta wuraren kwanan ‘yan gudun hijira ta hanyar shirin Solid, haɓaka yawan amfani da dabbobi ta hanyar shirin L-Press, gina hanyar mai nisan kilomita 126 daga magami-dangulbi-dankurmi-bagega-anka.”

Sauran ayyukan da za a ƙaddamar a cikin kasafin kuɗin 2025 sun haɗa da shirin NG-Cares na ƙarfafa ci gaban al’umma, gina cibiyar wasanni ta Gusau, gina titin Mallamawa – Zarummai – Bukkuyyum, gina sabuwar makarantar koyon aikin jinya da ungozoma ta Zurmi, kammalawa Cibiyar Siyayya ta Gusau da ke tsohon wurin shaƙatawa, da kuma gina titin kilomita 94 a Yandoton Daji-Doka-Yanwaren-daji-Hayin alhaji-Bedi-Yankuzo-Tsafe.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace
Labarai

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Tinubu
Manyan Labarai

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa
Labarai

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Next Post
Kasar Sin Na Adawa Da Danne Kamfanoninta Da Amurka Take Yi Bisa Fakewa Da Batun Tsaron Kasa

Kasar Sin Na Adawa Da Danne Kamfanoninta Da Amurka Take Yi Bisa Fakewa Da Batun Tsaron Kasa

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version