Bai wuce mako guda kenan da ayyana kanal Agbu Kefas a matsayin zababben gwamnan jihar Taraba ba amma shi da ubangidansa na siyasa, Gwamna mai barin gado Darius Ishaku, sun fara yakin cacar baki kan bashin albashin ma’aikatan gwamnatin jihar.
Kefas, a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai bayan nasarar da ya samu a zaben, ya yi alkawarin biyan duk wasu basukan albashin ma’aikata da gwamnatin Gwamna Ishaku ta rike musu, inda ya yi alkawarin biyan bashin cikin kwanaki 100 bayan rantsar da shi a 29 ga watan Mayu, 2023.
Sai dai Gwamna Ishaku a lokacin da yake mayar da martani ga alkawarin da Kefas ya yi, ya ce ma’aikatan jihar basu bin gwamnatinsa wani bashi Ballantana ya fara maganar cika wannan alkawari.
A wata sanarwa da aka raba wa manema labarai dauke da sa hannun mai baiwa gwamna Ishaku shawara kan harkokin yada labarai, Bala Dan-Habu, gwamnan ya nuna rashin jin dadinsa da ikirarin Kefas inda ya ce gwamnatinsa tana biyan ma’aikatanta albashinsu, babu wanda ke binta bashin sisi.