“Duk wata karramawar da za a yi wa Gwamnan Jihar Jigawa Namadi, tabbas ya cancanci a yi masa saboda a bayyane yake na irin yadda ya jajirce wajen gudanar da ayyukan raya kasa tun lokacin da ya dare karagar mulkin Jihar’’.
Bayanin haka ya fito ne daga bakin Babban sakataren watsa labarai na gwamna, Alhaji Hamisu Gumel a bikin karramawa da kamfanin LEADERSHIP ta gudanar a ranar Talata 8 ga watan Afrilu 2025, taron da aka gabagtar a tsohon dakin taro na fadar shugaban kasa da ke Abuja.
- Salah Ya Ƙulla Sabuwar Yarjejeniyar Shekaru 2 Da Liverpool
- Rayuwar ‘Yan Arewa Na Cikin Hadari, Yayin Da Gurbataccen Gishiri Ya Fantsama A Kasuwanni
Alhaji Hamisu Gumel ya kara da cewa, ayyukan raya kara da gwamnan ya gudanar sun karkade dukkan bangarorin rayuwar al’ummar jihar, musamman a bangaren bunkasa aikin gona, ilimi da bunkasa rayuwar matasa.
Ya kuma ce, ya tabbatar cewa, wannan karramawar za ta kara karfafa wa gwamnan wajen ci gaba ayyukan bunkasa rayuwar al’umma ba tare da wata matsala ba. Ya kuma shawarci masu rike da mukaman siyasa da sauran masu fada aji a Jihar Jigawa da su yi koyi da gwamnan wajen kawo wa gwamnati a bangaren bunkasa rayuwar al’umma a duk inda suke.
Taron dai ya samu halartar manyan yan siyasa da manyan ma’aikatan gwmanatin Jihar Jigawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp