Gwamnan jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris, ya amince da fitar da Naira Miliyan 27,500,000 (Naira miliyan Ashirin da bakwai da dari biyar) domin biyan kudin daliban makarantar lauyoyi a Nijeriya nan take da kuma rijistar ‘yan asalin jihar Kebbi 38 a makarantun lauyoyin Nijeriya.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Kwamishinan shari’a kuma Babban Lauyan Jihar, Dr. Junaidu Bello Marshal wacce aka rabawa manema labarai a Birnin Kebbi.
- An Nada Mambobin Hukumar Jindadin Alhazai Mutum 10 A Adamawa
- Batura Kirar Sin Sun Jawo Hankalin Kamfanoni Daga Duk Fadin Duniya
A cewar kwamishinan, dalibai 28 na Bar kashi na biyu za su karbi kudi naira 750,000 (Naira Dubu Dari Bakwai da Hamsin kadai) kowanne, yayin da daliban Bar kashi na daya za su samu kudi 650,000 (Naira dubu dari shida da hamsin kadai).
‘’ Amincewar Gwamnan ya zama wajibi ne a lokacin da hukumar kula da harkokin shari’a ta Nijeriya ta kara kudin zuwa Naira 476,000 (Naira Dubu Dari Hudu da Saba’in da Shida kacal) na Bar Part II da N353,000 (Naira Dubu Dari Uku da Hamsin Uku Kawai). da kuma Bar Part I”.
Babban lauyan gwamnati kuma kwamishinan shari’a, Dr Junaidu Bello Marshall, ya ce “a madadin daliban masu karatu a makarantun koyon aikin lauyanci da kuma harkokin shari’a ya godewa Gwamna Nasir Idris bisa wannan karamcin tare da tabbatar wa gwamnati kudirinsu na zama jakadu nagari a jihar.
Ya bayyana matakin gwamnan a matsayin cika alkawarinsa na samar da ingantaccen ilimi ga kowa da kowa.
Haka kuma idan dai ba a manta ba a shekarar 2017 ne karo na karshe da gwamnatin jihar Kebbi ta biya kudin makarantar koyon aikin lauya ta Nijeriya da kuma kudin rijistar ‘yan asalin jihar a shekarar 2017.