Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 100 ga kungiyar lauyoyi ta Nijeriya (NBA), domin gina sakatariyarta reshen jihar a Binrin Kebbi.
Ya bayar da wannan gudummawar ne a lokacin kaddamar da kwamitin gyaran fuska na shari’a, kwamitin gudanarwa da kuma kaddamar da wasu karin sassa biyu a ma’aikatar shari’a ta jihar.
- Sojojin Nijar Sun Kama Kasurgumin Dan Bindigar Da Ya Addabi Nijeriya, Kachallah Mai Daji
- Hauhawar Farashin Siminti: Majalisa Ta Bai Wa Dangote, BUA, Da Sauransu Wa’adin Kwanaki 14 Su Bayyana Gabanta
Ya kuma ba da tabbacin cewa, gwamnatinsa za ta samar wa alkalai da lauyoyi hanyoyin sufurin da suka dace, yana mai cewa ya samar da kudaden da za a gyara ababen hawansu.
“Ina girmama bangaren shari’a, kuma na kuduri aniyar kawo sauyi a bangaren domin a gaggauta gudanar da ayyukan adalci da kuma samun adalci ga kowa, ba tare da tsangwama ba.
Gwamnan ya yabawa majalisar dokokin jihar bisa gaggarumar amincewa da kudurin dokar sake fasalin shari’a tare da bayar da gudunmuwar kawo sauyi a fannin shari’a a jihar.