Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi ya amince da nadin Sakatarorin Kananan hukumomi 21 na jihar, bayanin hakan yana kunshe ne a cikin wata takardar sanarwar da ta fito ta hannun sakataren yada labarai na Gwamna Nasir Idris, Alhaji Ahmed Idris, a ranar Litinin.
A cewar sanarwar, Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG), Alhaji Yakubu Bala-Tafida, ya sanar da cewa Gwamna Nasir Idris ya amince da nadin Sabbin sakatarorin kananan hukumomi 21 na jihar Waɗanda suka hada da Muhammad Aliero, karamar hukumar Aliero; Dalhatu Muhammad, karamar hukumar Augie, da Mohammed Gawamba na karamar hukumar Bagudo.
- Kotu Ta Daure Wasu Mutane 3 Da Ake Zargi Da Kisan Wani Mutum A Gidan Yarin Adamawa
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 3, Sun Sace 26 A Zamfara
Sauran sun hada da Ahmed Zauro, karamar hukumar Birnin Kebbi; Mohammed Umar Bunza, karamar hukumar Bunza da kuma Hajiya Zainab, karamar hukumar Arewa.
Hakazalika, Umar Sama’ila, karamar hukumar Kalgo; Suleiman Koko, karamar hukumar Koko Besse; Buhari Bawa, karamar hukumar Maiyama; Aliyu Libata, karamar hukumar Ngaski; Aliyu Diri, karamar hukumar Sakaba, da kuma Aminiu Arzika daga karamar Shanga.
Har illayau, Akwai Abdullahi Kwakware, karamar hukumar Suru; Nasiru Dantani, karamar hukumar Yauri; Lawali Taget, karamar hukumar Argungu da kuma Abdurrahman Manga dsga karamar hukumar Zuru.
Sakataren Gwamnati jihar, Alhaji Yakubu Bala-Tafida, ya bukaci sabbin sakatarorin da aka nada su yi aiki tukuru don Samar da nasararori a kananan hukumominsu da kuma gudanar da ayyukansu bisa ga gaskiya da adalci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp