Gwamna Nasir Idris na Jihar Kebbi ya sanar da cewa, Gwamnatinsa za ta gina wani babban filin wasan kwallon guragu na zamani a jihar domin ganin Jihar ta yi kafada-da-kafada da takwarorinta a Nijeriya.
Ya ce, za a mika filin wasan ne ga shugabanni masu kula da masu bukata ta musamman a jihar.
- Ba Gwamnati Ce Kadai Za Ta Magance Yawan Barace-Barace Ba
- ‘Yansanda Sun Tsare Habashawa 24 A Dajin Kenya
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wasan karshe na lashe gasar kofin kwallon ta guragu da kungiyar kwallon ‘Para Soccer’ ta Kebbi ta shirya, inda kungiyar Jega Para ta lallasa kungiyar Kebbi para da ci 3-0 a filin wasa na Haliru Abdu da ke Birnin Kebbi.
A cewar Gwamnan, filin wasan zai kasance daya daga cikin mafi inganci a yankin Arewacin kasar nan domin bunkasa harkokin wasanni a jihar Kebbi.
Gwamna Nasir ya bayyana jin dadinsa da yadda ‘yan wasan ke buga kwallon, Inda yace, wasannin akwai Nishadantrawa sosai.