Gwamnan Jihar Binuwai, ya yi kira da a sake Shugaban haramtacciyar kungiyar gwagwarmayar kafa yankin Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, da ake tsare da shi a halin yanzu domin daukar matakin zaman lafiya da muhimmancin gaske a kasar nan.
Gwamna Ortom ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya amshi bakwancin wasu ‘yan asalin Igbo karkashin ‘American Veterans of Igbo Origin’ da suka kai masa ziyarar a Washington DC, da ke kasar Amurka ranar Laraba.
Ya ce, batun Kanu kalubale ne da ya shafi zamantakewa da siyasa don haka akwai bukatar tafiyar da lamarin cikin siyasa domin shawo kan kalubalen.
Gwamnan ya ce hatta mambobin Boko Haram da suka zama barazana ga tsaron kasa ana samun wadanda aka ‘yantasu har ma su koma cikin al’umma tare da zargi cewa har ma shiga aikin soja su na yi.
Gwamna Ortom ya ce akwai bukatar bai wa yankin Kudu Maso Gabas damar jin an tare da su ta hanyar sauraron kullin da ke ransu na ganin wariya ga wani bangare a kasar nan.
Ya jawo hankalin tsoffin ‘yan Igbo da suke zaure a Amurka da su cewa Nijeriya daya ce, ya duk duniya babu kasar da bata da kalubalen da ke damunta.
Ortom ya shaida wa kungiyar cewa mulkin Nijeriya zai dawo yankin Kudu Maso Gabas ne kawai idan al’ummar yankin suka jingine banbance-banbancensu waje guda suka hada kai domin cigabansu.
Gwamnan ya gode wa kungiyar a bisa gudunmawar da suke bayarwa ya kuma nemi da su cigaba da bada gudunmawarsu wajen kyautata zaman lafiya a Nijeriya.
Kungiyar a karkashin jagorancin Shugabanta Dakta Sylvester Onyia, da mataimakinsa Dakta Prince Joe Nduka.
Sauran mambobin da suka kai ziyarar sun hada da Dr Ofo, Kakakin kungiyar, tsohon Jakadan Nijeriya a Afirka ta Kudu Dr Mrs Ajulu.
Onyia ya jinjina wa Ortom a bisa kokarinsa, ya nuna cewa irin su Ortom Nijeriya take bukata a matsayin shugabanni. Ya ce, duk da suna kasar waje amma suna nazartar abubuwan da suke faruwa a Nijeriya.
Daga nan ya nuna fargana kan zaben 2023 da cewa matsalolin tsaro da suke faruwa a Nijeriya kada su kai ga kawo matsala ga babban zaben.