• English
  • Business News
Friday, October 31, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Raɗɗa Ya Raba Naira Miliyan 20 Ga Iyalan ‘Yan Sintirin Da Suka Rasu A Yaki Da ‘Yan Bindiga

by El-Zaharadeen Umar
2 years ago
Gwamna Radda

Gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Malam Dikko Umar Raɗɗa ya ware kuɗi naira miliyan 20 domin tallafawa iyalan ‘yan sintiri da suka rasa rayukansu a lokacin fafatawa da ‘yan bindiga.

Da yake ƙaddamar da bada wannan tallafi, sakataren gwamnatin jihar Katsina Alhaji Abdullahi Garba Faskari ya bayyana cewa, anyi wannan tsari da kyakkyawar niyya domin rage radadin rashin da iyalan jami’an tsaro da ‘yan sintiri suka yi.

  • Gwamnatin Tarayya Ta Shirya Don Fara Rigakafin Kansar Mahaifa

A cewar sa wannan ɗaya ne daga cikin tarin tsare-tsaren da wannan gwamnati take da shi na nuna kauna da tausaya wa ga iyalan waɗanda suka rasa iyalansu da kuma waɗanda suka samu raunuka.

LABARAI MASU NASABA

Rundunar Sojin Nijeriya Ta Shirya Wa Janar Musa Faretin Gama Aiki

Gwamnatin Tarayya Da Stellar Steel, Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Habaka Karafan Cikin Gida

Sakataren gwamnatin jihar Katsina ya ƙara da cewa wannan yana daga cikin alkawarin da gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa ya ɗauka akan wannan matsala ta tsaro wanda ya ce kullum da abin yake kwana da shi yake tashin.

“Idan jama’a ba su manta ba, gwamna Malam Dikko Raɗɗa ya bayyana cewa idan kuɗin jihar Katsina za su ƙare akan matsalar tsaro, to zai tunkare ta tsakaninsa da Allah, kuma ku shaida ne, kwana nan ya amince da kashe Naira biliyan dubu 7.8 akan wannan matsala.” Inji Faskari

Haka kuma ya yi kira ga jama’a da su taimakawa jami’an tsaro da bayanan sirri wanda zai taimaka wajan kawo ƙarshen wannan matsala, sannan ya ƙara jaddada cewa kofar wannan gwamnati a buɗe take domin ba

da shawara musamman akan sha’anin tsaro.

Shina yake jawabi, mai taimakawa Gwamna Raɗɗa akan waɗanda bala’in ‘yan bindiga ya shafa. Alhaji Sa’idu Ibrahim Danja ya bayyana cewa duk jami’an tsaron ‘yan sintiri sauransu gwamnati ke ɗaukar nauyin yi masu magani idan suka sami raunuka.

A cewar sa yanzu haka akwai jami’an tsaro guda 4 da jama’ar gari 32 da suke kwance a asibitin koyarwa ta Katsina da kuma asibitin Ƙashi kuma gwamnatin Malam Dikko Umar Raɗɗa ke ɗaukar nauyin yi masu magani.

Ya ƙara da wannan naira miliyan 20 da aka ware an tsara yadda za a rabawa iyalan waɗanda wannan lamari ya shafa su talatin da uku (33) inda ya ce kowace mutum za a baiwa iyalansa naira dubu 500 da kuma iyalan wani jami’in soja da ya rasa ransa za a bashi naira miliyan ɗaya .

” Haka kuma muna da jami’an tsaro guda goma da suka samu raunuka wanda kuma za a baiwa kowanne su Naira dubu ɗari biyu da hamsin (250) domin su cigaba da tallafawa iyalan su” inji

Daga ƙarshe ya bayyana cewa waɗannan kuɗaɗen da aka ba su ba wai diyya ba ce, tallafi daga gwamna Malam Dikko Raɗɗa kuma wata hanya ce ta ƙara ƙarfafa jami’an tsaro akan wannan aiki na sadaukarwa da suke yi ba dare ba rana.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Rundunar Sojin Nijeriya Ta Shirya Wa Janar Musa Faretin Gama Aiki
Labarai

Rundunar Sojin Nijeriya Ta Shirya Wa Janar Musa Faretin Gama Aiki

October 31, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP
Labarai

Gwamnatin Tarayya Da Stellar Steel, Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Habaka Karafan Cikin Gida

October 31, 2025
Ƴansanda Sun Kama  Wani Mai Wasa Da Bindiga AK-47 A Cikin Wani Bidiyo A Adamawa
Labarai

Ƴansanda Sun Kama  Wani Mai Wasa Da Bindiga AK-47 A Cikin Wani Bidiyo A Adamawa

October 31, 2025
Next Post
An Kama Masu Fataucin Kananan Yara A Ribas

Harin 'Yan Bindiga A Kauyen Dan-Umaru: 'Yansanda Sun Kwato Roka A Kebbi

LABARAI MASU NASABA

Rundunar Sojin Nijeriya Ta Shirya Wa Janar Musa Faretin Gama Aiki

Rundunar Sojin Nijeriya Ta Shirya Wa Janar Musa Faretin Gama Aiki

October 31, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

Gwamnatin Tarayya Da Stellar Steel, Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Habaka Karafan Cikin Gida

October 31, 2025
Ƴansanda Sun Kama  Wani Mai Wasa Da Bindiga AK-47 A Cikin Wani Bidiyo A Adamawa

Ƴansanda Sun Kama  Wani Mai Wasa Da Bindiga AK-47 A Cikin Wani Bidiyo A Adamawa

October 31, 2025
Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar

Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar

October 31, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa

October 31, 2025

Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda

October 31, 2025
Yan Nijeriya Na Ɗanɗana Kuɗarsu Kan Jinkirta Cire Tallafin Mai – Sarki Sanusi

Yan Nijeriya Na Ɗanɗana Kuɗarsu Kan Jinkirta Cire Tallafin Mai – Sarki Sanusi

October 31, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

Allah Ya Kai Manzon Allah (SAW) Muƙami Na Babban Yabo A Cikin Komai

October 31, 2025
Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare

Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare

October 31, 2025
Xi Jinping Ya Halarci Kwarya-Kwaryan Taron Shugabannin APEC Na 32 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Xi Jinping Ya Halarci Kwarya-Kwaryan Taron Shugabannin APEC Na 32 Tare Da Gabatar Da Jawabi

October 31, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.