Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya gargaɗi sabbin masu yin hidimar ƙasa (NYSC) da aka tura zuwa jihar da su guji shiga ƙungiyoyin sirri, da ayyukan siyasa, da kuma nuna kiyayyar addini a duk tsawon lokacin hidimarsu.
A cikin jawabin gwamnan, wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan jihar Abdulkadir Mamman Nasir, ya gabatar a yayin shirin gabatar da ƴan hidimar na rukunin A, na tsari na ɗaya, Gwamna Radda ya bayyana cewa wannan horon na farko wani muhimmin mataki ne a tafiyar hidimar ƙasa da mambobin NYSC ke yi.
- Masu Garkuwa Sun Nemi Fansar Miliyan 250 Kafin Su Saki Tsohon Shugaban NYSC, Janar Tsiga
- Minista Ya Nemi A Mayar Da NYSC Shekaru 2
Ya kara da cewa suna buƙatar su kasance cikin tsari na miƙa wuya ga alƙawarin da suka ɗauka yayin shiga aikin, yana mai tabbatar da cewa za su sami yanayi mai kyau a tsawon horon da za su yi, tare da ƙarfafa musu gwuiwa su shiga cikin dukkanin ayyukan sansanin.
Gwamna Radda ya jaddada mahimmancin kiyaye dabi’un NYSC da kuma ganin shekarar hidimar a matsayin daraja ga kasa, yana mai cewa su guji shiga dukkanin al’amuran da ka iya kawo rashin zaman lafiya a cikin al’umma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp