Gwamnan Jihar Katsina, Malam Umaru Dikko Radda, ya roƙi ƙasashen waje da ƙungiyoyin agaji na duniya da su tallafa wajen gina gidaje masu arha ga iyalan da rikicin ta’addanci da fashi da makami ya raba da muhallansu. Gwamnan ya yi wannan kira ne yayin wani shirin tallafa wa marasa galihu da aka shirya tare da Qatar Charity Nigeria a Katsina.
Ya bayyana cewa har yanzu akwai buƙatar ƙarin gidaje duk da cewa an riga an gina gidaje 152 tare da haɗin gwuiwar United Nations Development Programme (UNDP) don mazauna da suka rasa muhallansu sakamakon rashin tsaro. “Muna da fili da yawa a ƙananan hukumomi da suke buƙatar irin wannan taimako,” in ji shi, yana mai kira ga Qatar Charity da sauran abokan hulɗa na ƙasashen waje da su ƙara sa hannu don tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.
- Firaministan Sin Ya Isa New York Don Halartar Babban Taron Mahawara Na MDD Karo Na 80
- Babban Taron MDD Ya Zartas Da Kudurin Hadin Gwiwar MDD Da SCO
Radda ya jaddada cewa duk da muhimmancin taimakon ƙasashen waje, jihar Katsina ma tana ƙarfafa tsarin jin ƙai da zamantakewa. Ya ce gwamnatinsa na saka jari a fannin koyon sana’o’i, da tallafin kuɗi ga ƙananan ƴan kasuwa, da shirye-shiryen a ƙauyuka don rage talauci da kuma ƙarfafa haɗin kai.
Wannan kiran nasa ya zo ne a lokacin da aka raba babura, da injinan ɗinki, da injinan niƙa ga ɗaruruwan gwauraye, da kuma marayu, da marasa galihu a jihar.
Gwamnan ya yaba wa Qatar Charity Nigeria bisa wannan tallafi, yana mai bayyana shi a matsayin hanya ta tallafa wa rayuwa da kuma kawo sauyi. Ya kuma shawarci waɗanda suka amfana da kayan da su yi amfani da su yadda ya kamata domin inganta rayuwarsu, yana mai nanata ƙudirin gwamnatinsa na tabbatar da cewa kowane ɗan jihar ba a bar shi a baya ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp