Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda ya ba da umarnin rufe makarantun koyar aikin lafiya masu zaman kansu a jihar da ba su da rajista.
Mai bai wa gwamnanan shawara kan harkokin lafiya, Alhaji Umar Mamuda ya bayyana haka wurin taron manema labaru da aka gudanar a ma’aikatar yada labaru da al’adu a Katsina.
Ya ce bincike kwanan nan da ma’aikar lafiya da gwamnatin jihar suka gudanar ya zamo abin damuwa bisa yawan makarantu masu zaman kansu da ba su da rajista.
A cewarsa, wasu makarantun ba su cika ka’idojin da za su bude makarantun kiwon lafiya masu zaman kansu ba a jihar, wanda hakan yake da hatsari ga lafiyar al’umma.
Ya bayyana umarnin rufe makarantun zai ci gaba da aiki har sai an gama tantancewa da kuma sake wa makarantun rajista. Ya bukatar masu makarantun su je ma’aikatar lafiya ta jihar domin a tantance su.