Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda ya tallafa wa mata sama da 8,000 naira miliyan 4, wadanda yaransu suka samu allurar rigakafi a jihar.
An yi rabon kudaden ne a lokacin kaddamar da cibiyar allurar rigakafi da rabon babura 163 ga cibiyoyin kiwon lafiya da ya gudana a hukumar kula da lafiya matakin farko da ke Katsina.
- Shekara 64 Da Samun ‘Yanci: Maimakon Biki, Jajantawa Ya Kamata A Yi – ‘Yan Nijeriya
- APC Ta Lalata Nijeriya, PDP Kuma Matacciyar Jam’iyya Ce — Kwankwaso
Gwamna Radda ya yi alkawarin ci gaba da hada hannu da kungiyoyin ba da tallafi da masu ruwa da tsaki don tabbatar da ganin shirin ya dore.
Sannan ya yi kira ga iyaye a jihar da su bari a yi wa ‘ya’yansu allurar rigakafi, wanda aka shirya yi wa yara sama da miliyan 3 rigakafin ‘yan kasa da shekaru biyar.
Tun da farko, shugaban hukumar kula da lafiya matakin farko ta Jihar Katsina, Dakta Shamsuddeen Yahaya ya roki gwamnan jihar da ya aiwatar da tsarin cike gibin ma’aikatar kiwon lafiya a jihar.
Ya ce aiwatar da hakan zai samar da karin jami’an na kiwon lafiya don cike gibin gurbin da wasu suka ajiye aiki a bangaren na kiwon lafiya.
Shi ma a nasa jawabin, kwamishinan kiwon lafiya, Alhaji Musa Adamu Funtua ya yaba wa kokarin gwamna kan tsarin maido da martabar bangaren kiwon lafiya a Jihar Katsina.