ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, July 16, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

A Kawo Karshen Mace-mace A Hanyoyinmu

by Leadership Hausa and Sulaiman
2 years ago
mace-mace

Hanyoyin Nijeriya sun zama hanyoyi dake da ban tsoro masu sanadiyar rasa rayukan jama’a. Daga cikinsu akwai na kwana kwanan nan, hatsarin da a ka yi a Kaduna inda mutum arba’in suka rasu a kan hanyar su ta zuwa wurin bilin maulidi.

Motar da suke ciki ne ta yi taho mu gamu da wata tankar mai a hanyar Saminaka kta kramar hukumar Lere, a Jihar Kaduna.

ADVERTISEMENT
  • Kaso 40 Na ‘Yan Nijeriya Na Samun Wutar Lantarki Fiye Da Awa 20 A Kowace Rana — Minista
  • Kirkirar Kimiyya Da Fasaha Ta Kasar Sin Na Sa Kaimi Ga Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

Kwanaki kadan kafin wannan, wani mummunan hatsarin da ya afku a Jihar Neja inda ya yi sanadiyyar rasuwar mutum arba’in da takwas bayan wata takar mai ta hade da tifa wanda ya yi sanadiyyar mummunar fashewa.

Wata daya kafin wannan nan kuma, an samu hatsari  daban-daban a Jihar Oyo da Ogun inda mutum talatin da bakwai da ashirin da biyar suka rasu a ranadaya a babbar hanyar Ibadan zuwa Legas.

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Dauda Lawal Zai Gabatar Da Jawabi A Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Jami’ar FUE Zariya

Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci A Tura Ƙarin Sojoji da ’Yansanda Zuwa Benuwe

Wannan ba kawai kididdiga ba ne, wannan yana nuna  yadda mutane ke rasa rayukansu ta hanyar da za a iya kiyayewa.

Duk da yadda yawan adadin mutanen da suke rasuwa ta hanyar hatsari ya ragu a shekara 2023, da kimanin mutum 5,081 idan a ka kwatanta da mutum 6,456 da suka rasu a shekarar 2022, kamar yadda hukumar kula da hanyoyi a Nijeriya ta bayyana.

Nijeriya tana cikin kasashe masu yawan mutuwa a kan tituna a duk duniya da kaso 33.7 a cikin mutum 100,000 wanda ya wuce yadda ya kamata wato kaso 17.4.

Mu dawo dashi daidai, kason da ya kamata ya tsaya a duniya shi ne, 17.4 duk mutum 100,00. Inda kasar Zimbabwe take kan gaba da kimanin mutuwar mutane 74.5 duk daga cikin mutum 100,000.

Dililan da suke janyo wannan mace-macen a kan hanyoyi sannannu ne kuma kididdigaggu. Gudun wuce  kima  shima yana kan gaba inda direbobi suke wuce iyakan da aka sanya domin samun riba mai yawa musamman a motocin haya.

Tukin ganganci, gajiya, da kuma oba lod a motoci da kuma tuki cikin dare ne suke kara girmama hatsarin.

A ‘yan shekarun nan, yawan anfani da wayar hannu a lokacin tuki ya kara munana lamarin. Inda direbobin da hankalinsu ya dauke suke jawo hatsari. Ko ta hanyar daukar waya, tura sakonni, ko kuma duba shafukan sada zumunta, wadannan abubuwan da ke dauke hankali sun nuna suna da hatsari sosai.

Lalacewar hanyoyin Nijeriya kuma yana kara hauhwar matsalar. Manyan tituna sun lalace da ramuka, kuma ba tare da alamun hanya masu kyau ba inda hatta direbobi masu kiyayewa ke iya fadawa cikin hatsari.

Duk da ana yawan zargin direbobi masu zaman kansu, lalacewa da kuma rashin gyara da kuma kawo karshen lalatattun hanyoyi na cikin abubuwa masu tada hankali.

Abun takaicin shi ne masu kula da dokokin hanya sun mayar da hankalinsu wajen kananan abubuwan da basu da muhimmanci kamar takardun mota, inda suka mai da hakan hanyar samun kudi maimakon wajen kare rayukan mutane.

Tsofaffin hanyoyin magance hadurran da muke amfani dasu sun gaza. A wasu kasashen duniya kimiyya ya taka rawar gani wajen magance mace mace a hanyoyi ta hanyar anfani da kamarorin duba gudu da kuma na’urorin agajin gaggawa. A Nijeriya, wannan ci gaban ya yi karanci, hakan  abin yake barin hanyoyin a lalace fiye da yadda ya kamata su zama.

Ilimin direbobi shi ma babban abin lura ne. Hanyar samun lasisi a Nijeriya cike yake da cin hanci, hakan yake barin direbobin da basu cacanta ba suna samun lasisi ba tare da horon da ya dace ba. Ya kamata a sauya tsarin samun lasisin, a kuma maida hankali wajen ilmantarwa, gwaji da kuma horar da direbobin.

Mace-macen rayuka a kan hanyoyi na tada hankali. Hatsari a hanyoyi ya zama hanya na biyu da yake kawo mace mace wanda ya wuce ayyukan Boko Haram da ‘yan ta’adda. Duk da ana maida hankali wajen su wadancan kalubalen, mace-macen da a ke samu a hanyoyi su ma suna  tayar da hankali.

Hadarurruka na da tasiri a fannin tattalin arziki. Asibitoci, sun riga sun cika kuma babu isasshen kayan aiki ga majinyantan hatsarruka a kwance. Iyalai na fuskantar barazana ta hanyar rasa jigogin iyalin, kasuwanci na samun tsaiko wajen samun kayayyaki da kuma tafiyar ma’aikata.

Wadannan su ne hanyoyin da ta kamata gwamnati ta dauka, na farko,  zuba jari da kuma manyan ayyuka a hanyoyi. Manyan hanyoyi na bukatar gyara a kai a kai, dole a gyara ramuka, a samar da wuta,da kuma alamun nuni a hanyoyi. Wadannan ci gaban za su iya samar da gagarumin sauyi wajen kare afkuwar hadurra.

Kimiyya da fasaha na taka rawar gani wajen kiyaye hadurra. A samar da kamarori, musamman a wajen da suke da hadari, wannan zai rage guje guje da kuma tukin ganganci. A kuma samar da wajen samar da agajin gaggawa a kusa da manyan hanyoyi su zama a shirye wajen kawo dauki idan an samu hadurra.

Tsaurara dokin tuki a hanyoyi shima wani babban hanya ce. Hukumar Kare Hadurra da sauran masu sa ido dole a samar masu da kayan aiki kuma a sa masu ido domin tabbatar da suna aiki yadda ya kamata. Wannan ya hada da kama masu gudun ganganci, masu shaye shaye yayin tuki, da kuma masu yin wasu abubuwa yayin da suke tukin. A samar da tara ga duk wanda ya karya dokokin ya zama mai tsanani saboda ta zama izinina ga saura. Sannan kuma a dauki mummunan mataki a kan masu nanata laifi.

Ilimin direbobi na da matukar muhimmanci, wannan hanyar samun lasisin dole a canza shi da tsari mai kyau wanda kuma za a tabbatar da bin doka a ciki. Ya zama direbobi na fuskantar tantancewa, da kuma horo wa da zai sanya masu al’adun tuki a tattare dasu. A kuma tsananta wayar da kan jama’a masu amfani da hanyoyi  akan hadurra da kuma yadda ganganci ke jawo aukuwarsu.

mace-mace
Leadership Hausa
Website |  + posts Bio
  • Leadership Hausa
    Tallafa Wa Yara Masu Buƙatu Na Musamman Shi Ne Burina
  • Leadership Hausa
    Dole Mata Su Rungumi Sana’o’i Domin Tsira Daga Takaicin Zamani —Ramatu Bello
  • Leadership Hausa
    Batun Dakile Shan Taba Sigari A Tsakanin Yara A Nijeriya
  • Leadership Hausa
    Har Yanzu Akwai Sauran Rina A Kaba Game Da Makomar Yara A Nijeriya
mace-mace
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Binciken CGTN: Amfanar Da Kowa Da Kowa Shi Ne Ainihin Alherin Da Fasahohin Kwaikwayon Tunanin Bil Adama Suka Kawo
  • Sulaiman
    Sin Ta Yi Kira Da A Kafa Tsarin Jagorantar Muhimman Ma’adinai Ga Sauyawa Zuwa Amfani Da Makamashi Mai Tsafta
  • Sulaiman
    Gwamna Dauda Lawal Zai Gabatar Da Jawabi A Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Jami’ar FUE Zariya
  • Sulaiman
    Neman Raba-Gari Da Sauran Kasashe Zai Kawo Mummuann Tasiri Ga Bangarorin Da Abin Ya Shafa

MASU ALAKA

Gwamna Dauda Lawal Zai Gabatar Da Jawabi A Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Jami’ar FUE Zariya
Labarai

Gwamna Dauda Lawal Zai Gabatar Da Jawabi A Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Jami’ar FUE Zariya

July 15, 2026
Sabbin Ministoci
Labarai

Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci A Tura Ƙarin Sojoji da ’Yansanda Zuwa Benuwe

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 
Labarai

Atiku Ya Nuna Damuwa Kan Kasafin Naira Biliyan 6.44 Don Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026

July 15, 2026
Next Post
Wakilin Sin: Ya Kamata A Kiyaye Da Karfafa Gudummawar MDD A Fannin Yaki Da Ta’addanci

Kevin Kelly: AI Na Iya Taimakawa Wajen Cimma Burin “Koyar Da Dalibai Da Kwazonsu”

Kevin Kelly: AI Na Iya Taimakawa Wajen Cimma Burin “Koyar Da Dalibai Da Kwazonsu”

July 15, 2026
Gwamna Yusuf Ya Bai Wa Masu Kula Da Akwatinan Zaɓe Na APC Filaye 1,540 Da Tallafin Miliyan 100

Gwamna Yusuf Ya Bai Wa Masu Kula Da Akwatinan Zaɓe Na APC Filaye 1,540 Da Tallafin Miliyan 100

July 15, 2026
Sabbin Ministoci

Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci A Tura Ƙarin Sojoji da ’Yansanda Zuwa Benuwe

July 15, 2026
GDPn Sin A Rabin Farko Na Shekarar 2026 Ya Karu Da Kashi 4.7% Idan Aka Kwatanta Da Na Kwatankwacin Lokacin Bara

GDPn Sin A Rabin Farko Na Shekarar 2026 Ya Karu Da Kashi 4.7% Idan Aka Kwatanta Da Na Kwatankwacin Lokacin Bara

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 

Atiku Ya Nuna Damuwa Kan Kasafin Naira Biliyan 6.44 Don Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026

July 15, 2026
Masana Kandagarkin Cututtuka Na Sin Sun Tashi Zuwa Kasar Uganda Don Aikin Hadin Gwiwar Magance Cutar Ebola

Masana Kandagarkin Cututtuka Na Sin Sun Tashi Zuwa Kasar Uganda Don Aikin Hadin Gwiwar Magance Cutar Ebola

July 15, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.