Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya mayar wa iyalan marigayi Janar Sani Abacha fili guda biyu da ke wurare biyu daban-daban a cikin garin Kaduna shekaru biyu bayan tsohon gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufai ya kwace su.
Filayen guda biyu masu lamba 9 Abakpa GRA, Kaduna, mai girman 2284(sqm), wanda ke dauke da takardar shaidar zama ta jihar Kaduna 30575 da kuma mai lamba No. 1 Degel Road, Ungwan Rimi, GRA, Kaduna, mai girman 3,705 (SqM), wanda ke dauke da shaidar zama jihar Kaduna 11458.
- Babbar Kotun Tarayyar Kaduna Ta Sa Ranar Sauraron Karar Wasu Mahajjata Kan Hajjin 2024
- Gwamnatin Tarayya Ta Sauya Sunan Jami’ar Abuja Zuwa Jami’ar Yakubu Gowon
Lauyan iyalan Abacha, Reuben Atabo (SAN) ya shaida wa manema labarai cewa, an kwace hakkin mallakar filayen guda biyu ne a shekarar 2022 a karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai.
Sai dai a cikin ikon sa, Gwamna Sani acikin wasiku biyu masu kwanan wata 10 ga Disamba 2024, ta hannun Mustapha Haruna, (Deed Registrar) a madadin Darakta Janar na Hukumar Kula da filaye na Kaduna (KADGIS) ya maido da hakkin mallakar filayen guda biyu amma ya nemi a biya kudin harajin ƙasa.
An aika da wasikun ne zuwa ga Mohammed Sani Abacha, care R.O Atabo, SAN & Company.