Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya rattaba hannu kan kudirin dokar da ta bai wa jihohi damar samar da wutar lantarki tare da rarrabawa al’ummar jihar.
Rattaba hannu kan dokar samar da wutar lantarki ta jihar Nasarawa 2024, wani muhimmin mataki ne na ganin an samar da dokar da ake bukata domin gudanar da ayyukan samar da wutar lantarki a jihar.
- Atiku Ya Yi Allah-wadai Da Karramawar Da Sojoji Suka Yi Wa Seyi Tinubu
- Manyan Makarantun Bauchi Sun Tsunduma Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani
Takardar doka mai taken: “Dokar samar da wutar lantarki ta Jihar Nasarawa 2024”, Gwamna Sule ne ya rattaba mata hannu a wani taro a gidan gwamnati da ke Lafia, babban birnin jihar.
LEADERSHIP ta rahoto cewa, gyaran kundin tsarin mulkin Nijeriya da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya wa hannu a shekarar 2023 ya bai wa jihohi 36 ikon samar da wutar lantarki tare da rarrabawa.
Da yake jawabi a lokacin da ya rattaba hannu kan dokar, Gwamna Sule ya ce, dokar wutar lantarki da tsohon shugaban kasa ya amince, za ta bai wa jihar Nasarawa damar amfani da makamashin ruwa da hasken rana da ke da yawa a jihar.
Ya ce, gwamnatinsa za ta kawo kwararrun masana, wadanda za su sa a cimma nasarar shirin samar da wutar lantarkin da yardar Ubangiji.