Gwamnan jihar Sokoto Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ya yi ta’aziya ga Gwamna Abubakar Atiku Bagudu da ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya Abubakar Malami (SAN) bisa rasuwar wasu jiga-jigan ‘ya’yan jihar guda hudu a wani hatsarin mota a daren Alhamis akan titin Yauri-Birnin Kebbi akan hanyar su ta dawowa daga Abuja.
Marigayan dai sun hada da, Dokta Hussaini Abdullahi-Goro, masanin harhada magunguna; Aliyu Tanko-Nassarawa Wanda aka fisani da (Aliyu Kwara), tsohon dan majalisar dokokin a jihar Kebbi; Yakubu Magaji-Alwasa da Abdullahi Abubakar-Dalijan.
Gwamna Tambuwal a lokacin da ya isa Birnin Kebbi, ya sauka a gidan gwamnati da ke Birnin Kebbi tare da yin ta’aziya da kuma jajantawa Gwamnan Jihar.
Bayan haka gwamnonin biyu sun gana da ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami (SAN) inda suka wuce gidan daya daga cikin marigayin, Aliyu Tanko Nassarawa (Aliyu Kwara), wanda tsohon dan majalisar dokokin jihar Kebbi ne domin ta’aziyya ga iyalansa.
Haka Kuma Gwamna Tambuwal a cikin sakon ta’aziyyar ya bayyana marigayin a matsayin ’yan uwa masu tawali’u kuma babban rashi ne ba ga jihar Kebbi kadai ba har ma da Jihar Sakkwato da kanta.
Kazali ka ,yayi addu’ar Allah ya gafarta musu, ya kuma baiwa iyalansu hakurin jure rashin.
Gwamna Abubakar Atiku Bagudu da Ministan Shari’a kuma Atoni-Janar na Tarayya, Abubakar Malami (SAN) sun nuna matukar godiya ga Gwamna Tambuwal bisa ziyarar ta’aziyyar da ya kai masa, inda suka yi addu’ar Allah ya kai shi gida lafiya.