Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya fito fili ya ki amincewa da magajinsa a ofis, Gwamna Uba Sani, da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, a matsayin abokansa.
Ya ce, duk da cewa su biyun sun kasance abokansa a baya, amma a yanzu kowa yana da abubuwan da ya saka gaba.
- Kasar Sin Ta Cimma Burin Magance Gurbatar Yanayi A Shekara Ta 2024
- Sin Ta Ki Amincewa Da Takardar Manufofin Zuba Jari Da Amurka Ta Gabatar
El-Rufai, wanda ya bayyana hakan a daren ranar Talata, yayin da yake magana a shirin ‘PrimeTime’ na gidan talabijin na ‘Arise News Channel’ wanda Charles Aniagulu ya jagoranta, ya kuma ce zabe mai zuwa na shekarar 2027 zai nuna wadanda yake tare da su da wadanda basa tare a Siyasa.
Ya kuma zargi NSA da nuna sha’awar tsayawa takarar shugaban kasa a 2031, don haka yake kokarin kawar da duk wanda zai zamar masa kalubale a kan hanyarsa.
Cikakken bayani na nan tafe…
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp