Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya kaddamar da ginin titin Anchau-Gadas-Palla mai tsawon kilomita 21.7 a kananan hukumomin Kubau da Ikara na jihar.
Da yake jawabi a Anchau da ke karamar hukumar Kubau, gwamnan ya ce hanyar za ta hade kauyuka 32 a fadin kananan hukumomin biyu.
Sanata Uba Sani ya yi nuni da cewa, hanyar idan aka kammala ba wai kawai ta saukaka zirga-zirgar jama’a ba ne, har ma za ta habaka jigilar kayan amfanin gona daga gonaki zuwa kasuwanni, wanda hakan zai habaka ci gaban karkara da tattalin arzikin cikin gida.
Ya jaddada cewa, tsaron rayuka da dukiyoyi da habbaka tattalin arziki shi ne babban abin da gwamnatinsa ta sa gaba, sannan ya yi alkawarin daukar mataki kan duk wasu masu shirin addabar zaman lafiyar jihar.
Anasa bangaren, Shugaban karamar hukumar Kubau ya nuna jin dadinsa ga gwamnatin jihar kan zaben kananan hukumominsu a matsayin wadanda za su ci gajiyar irin wadannan ayyukan a wani bangare na murnar cika kwanaki 100 na sabuwar gwamnatin jihar.