Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya amince da aiwatar da cikakken tsarin biyan albahin Likitoci da ke aiki a karkashin ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar Kaduna (CONMESS) da aka inganta tun a shekarar 2014.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a ranar Lahadi, 3 ga Satumba, 2023 kan cika kwanaki 100 akan karagar mulki.
Ya yi amfani da damar wajen bayyana batutuwa da dama a sassa daban-daban, musamman harkokin kiwon lafiya, tsaro da ci gaban ababen more rayuwa da dai sauransu.
Ya ce, bisa shawarar kwamitin da shugaban ma’aikatan jihar Kaduna ya jagoranta, bayan tattaunawa da likitocin da suka shiga yajin aiki a watan Agustan 2023, sun bayyana cewa, Likitocin da ke aiki a ma’aikatar lafiya ta jihar Kaduna ana biyansu kashi 75% na tsarin CONMESS na shekarar 2014, yayin da takwarorinsu da ke aiki a asibitin koyarwa na Barau Dikko ana biyansu kashi 100% na CONMESS.
“Sabida haka, daga watan Satumba na 2023, mun amince a fara biyan Likitoci dukkansu kashi 100% na tsarin CONMESS. Muna fata, wannan zai kara wa Likitocin karfin guiwa kuma zai janyo sabbin Likitoci zuwa jihar Kaduna.” inji Gwamna Uba Sani.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa, an amince da ci gaba da daukar Likitoci 89 domin magance karancin Likitoci da aka gano tun a shekarar 2017, kamar yadda kwamitin ya ba da shawarar.