Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana tsare-tsaren gwamnatinsa na samar da zaman lafiya, magance matsalar rashin tsaro da tabbatar da aminci a fadin jihar Kaduna.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya kasance babban bako a wajen wani taro da kungiyar zaman lafiya ta Kaduna ta shirya a jami’ar jihar Kaduna, domin tunawa da ranar zaman lafiya ta duniya ta 2023.
- Gwamna Uba Sani Ya Nada Sabbin Manyan Sakatarori 19 Da Kara Wa’adin Wasu 7
- Harin Cocin Kafanchan: Wasu Ne Ke Yunƙurin Kitsa Rikicin Addini, Za Mu Damƙo Su – Uba Sani
Gwamnan wanda ya samu wakilcin mai ba shi shawara na musamman kan zaman lafiya da magance rikice-rikice, Atiku Isaac Sankey ya wakilce shi a wajen taron, ya ce, gwamnatin Kaduna na kara inganta ginshikin tsaro a jihar, wanda hakan ya sa ta kara daukar karin ‘yan banga 7,000 akan ‘yan banga 2,000 da ake da su a fadin jihar domin taimakawa jami’an tsaro a jihar.
Ya kara da cewa, gwamnatin za ta zurfafa tattaunawa a tsakanin al’ummomi daga bangarori daban-daban a jihar ta hanyar gano wa da magance matsalolin da ke bijiro wa.
Ya kara da cewa, gwamnatin Gwamna Uba Sani tana yaba wa da irin rawar da sarakunan gargajiya ke takawa wanda hakan ke inganta muhimmiyar alaka tsakanin gwamnati da jama’a. Lallai, iliminsu da hikimarsu na da matukar amfani wajen wanzar da zaman lafiya.