Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya wakilci Nijeriya a taron koli na biranen Asia wanda ya gudana a ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), inda ya gabatar da kudirorin sauyin ci gaban Kaduna.
Taron wanda ya samu halarcin manyan baki daga ƙasashe sama da 150 ciki har da gwamnoni, shugabannin birane, da jagororin kasuwanci daga nahiyoyin Asiya, Fasifik da Turai, da kuma Afirka.
- Makarantar Kogi Poly Ta Bankaɗo Masu Ƙirƙirar Takardun Kammala Karatu na Bogi
- Allah Ya Kai Manzon Allah (SAW) Muƙami Na Babban Yabo A Cikin Komai
Taron, wanda taken wannan shekarar mai taken : “Haɗin Gwiwa. Ƙarfafawa. Sauyi.”, ya kasance wani dandalin musayar ra’ayoyi da dabarun ci gaba tsakanin shugabannin birane domin samar da ci gaban birane mai ɗorewa tare da haɗin kai.
A jawabinsa yayin taron, Gwamna Sani ya gabatar da kasida mai taken: “Gina Haɗin Gwiwa Domin Ci Gaban Kowa”, inda ya bayyana yadda Jihar Kaduna ke ci gaba da samun nasara a fannoni da dama kamar gyaran birane, bunƙasa noma, da tsarin tallafiwa jama’a.
Gwamnan Ya ce tsarin ci gaban jihar yana dogara ne kan faɗaɗa damar tattalin arziki da kare marasa ƙarfi, da ƙarfafa jama’a su samu nasara a rayuwarsu.
Gwamna Uba Sani, ya kuma halarci shirin baje koli na birnin Dubai mai taken : “Sauya Arewa a Nijeriya: Jagoranci, Ƙirƙira, da Tasirin Zamantakewa”, inda nan ma ya jaddada cewa jagoranci mai nagarta da amfani da fasaha a mulki suna da matuƙar muhimmanci wajen buɗe damarmaki ga mutane da birane.
A yayin taron, Gwamnan ya gudanar da wata ganawa ta musamman da Marwan Bin Galita, Darakta Janar na birnin Dubai inda suka tattauna batutuwan haɗin gwiwa a fannin kirkirar makamashin sharar gida da kula da sharar gida ta zamani, da kuma tsare-tsaren gine-ginen birane na zamani.
A ganawar, duk Bangarorin biyu sun amince da zurfafa haɗin kai a fannin fasaha da musayar ƙwarewa domin tallafawa sauyin jihar Kaduna zuwa tattalin arzikin mai ɗorewa.
Gwamna Sani ya bayyana cewa halartar Jihar Kaduna a taron (APCS 2025) na nuna shirin jihar na shiga sahun ƙasashen duniya wajen yin haɗin kai, ƙirƙira, da zama abin koyi a fannin ci gaba mai ɗorewa da ci gaban kowa da kowa a fadin Nijeriya da ma duniya baki ɗaya














