A kokarin ganin an tsaftace aikin hajji, Gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa wani kwamiti da zai binciki matsalolin da suka dabaibaye gudanar da aikin hajji a fadin jihar.
Gwamnan jihar, Malam Uba Sani shi ne ya bayyana haka a wajen rufe gasar karatun Alkur’ani na jihar, wanda aka gudanar a Kaduna.
- Kwace Wa NNPP Zaben Kano Na Iya Haddasa Tashin Hankali A Afrika – NNPP
- An Kammala Aikin Bututun Karkashin Ruwa Na Sabuwar Hanyar Sin Da Ta Ratsa Teku
A cewarsa, kwamitin zai duba yadda ya kamata kan matsaloli daban-daban da suka daibaye ayyukan hajji tare da samar da mafita.
Gwamna Uba Sani, ya nuna rashin gamsuwarsa dangane da yadda aka gudanar da aikin hajjin da ya gabata a jihar. Ya ce muhajjatar jihar sun fuskanci matsaloli masu yawan gaske a kasa mai tsarki wanda hakan bai ji dadi ba.
Ya kuma bayar da tabbacin cewa aikin hajjin bada zai zama mai tsafta, wanda hakan ne ya sanya ya kafa kwamiti da zai sanya ido a bangaren.
A kwanan ma, Sarkin Zazzau, Nuha Bamalli, wanda shi ne Amirul Hajji na jihar, ya bayyana damuwarsa dangane da yadda aka gudanar da aikin hajjin da ya gabata, musamman ganin yadda muhajjatan jihar suka tagayyara a kasa mai tsarki, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce a jihar.
Gwamna Uba Sani ya ba da tabbacin ci gaba da bayar da fifiko wajen ciyar da harkar addini a gaba a jihar. Yana mai cewa shi da kansa zai fara jagorantar ‘yan majalisarsa wajen gudanar da karatun Alkur’ani a ko da yaushe bisa muhimmanci da darajar da yake tattare da karanta Alkur’ani mai girma.