Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya kammala fentin babban titin da ya ratsa Unguwar Sarki, unguwar tsohon gwamna Nasir El-Rufai, wanda aka dade da yin watsi da shi.
Unguwar Sarki na daga cikin unguwannin da ke ƙaramar hukumar Kaduna ta Arewa, kuma titin na da matukar muhimmanci wajen haɗa al’umma da muhimman wurare.
Sarkin Unguwar, Alhaji Ibrahim Isa, ya bayyana a lokacin bikin ƙaddamar da titin cewa gwamnoni da suka gabata sun yi biris da titin, wanda hakan ya jefa al’umma cikin ƙura da cunkoso. Ya ce mutane da dama sun daina shiga unguwar saboda lalacewar titin.
Ya bayyana cewa titin yana kaiwa har gidan Sultan na Sokoto da ke Kaduna, kuma bayan kammala aikin, Unguwan Sarki ta dawo da kuzari, harkokin kasuwanci ma sun farfaɗo.
Shugaban matasan unguwar, Aliyu Faruk, ya roƙi gwamnan da ya samar da ruwan famfo, domin an lalata bututun ruwa a lokacin aikin fasalin gari (Urban Renewal Programme).
Gwamna Uba Sani ya amsa da cewa gwamnati ta kashe sama da Naira biliyan 100 cikin watanni shida don magance matsalar ƙarancin ruwa a faɗin jihar, tare da alƙawarin cewa za a maye gurbin dukkan kayan aikin da suka lalace. Ya ƙara da cewa an riga an kashe sama da Naira miliyan 400 wajen gyara da maye gurbin bututun ruwa da aka lalata, kuma kafin ƙarshen shekara Kaduna za ta fara samun ruwa ba tare da katsewa ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp