Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya amince da nadin Dakta Abdulkadir Muazu Mayere a matsayin sakataren gwamnatin jihar Kaduna. Ya maye gurbin Mallam Balarabe Abbas Lawal wanda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar a matsayin ministan muhalli. Nadin Dakta Mayere ya fara aiki nan take.
Dakta Abdulkadir Muazu Mayere, babban sakatare ne na gwamnatin tarayya mai ritaya. A matsayinsa na babban sakataren gwamnatin tarayya, ya yi aiki a manyan ma’aikatu a lokuta daban-daban, kamar ma’aikatar ma’adinai, ma’aikatar noma da raya karkara, dukkan ma’aikatun biyu, an samar da su ne game da dabarun ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin Nijeriya da yaki da fatara da yunwa.
- Rashin Tsaro: Gwamnatin Sokoto Ta Kafa Kwamitin Samar Da Jami’an Tsaron Jihar
- Halittun Da Ba Sa Mutuwa Da Masana Kimiyya Ke Mamaki
Ya yi aiki na tsawon shekaru 32 a ma’aikatun gwamnatin tarayya, inda ya fara daga matsayin Likita (II) har ya zama Darakta a fannin likitanci a bangaren wasanni a ma’aikatar matasa da wasanni ta tarayya a shekarar 2011. An nada shi babban sakataren gwamnatin tarayya a shekarar 2017.
A halin yanzu, Dakta Mayere, yana aiki a matsayin babban mai ba da shawara na kasa ga Hukumar Abinci da Aikin Noma (FAO) ta Majalisar Dinkin Duniya a shirin “Hand in Hand Initiative in Nigeria,” yana aiki tare da hukumomin gwamnatin tarayya da na wasu jihohi kan cimma nasarar shirin SDG #1 da SDG#2.
Gwamna Uba Sani, na fatan sabon sakataren gwamnatin zai yi amfani da kwarewarsa wajen ganin an cimma buri na wannan gwamnati mai dorewa. Ya yi fatan Allah ya yi masa jagora da kariyarsa a sabon aikinsa.