Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya amince da nadin sabbin sakatarorin dindindin guda 19 tare da tabbatar da 7 daga cikin tsoffin sakatarorin dindindin.
Sabbin Sakatarorin Dindindin da ma’aikatun da aka tura su, ga su kamar haka:
- Mukhtar Abdullahi – Ma’aikatar ci gaban Wasanni
- Dorcas Inti Benjamin Iliya – Ma’aikatar Ayyuka da ci gaban Al’umma
- Jummai C. Bako – Tsare-tsare karkashin ofishin Shugaban Ma’aikata
- Jummai A. Danazumi Esq. – Ma’aikatar Shari’a
- Rabiu Yunusa – Ma’aikatar Gidaje da raya birni
- Ibrahim Sanusi – Hukumar Ma’aikatar kananan hukumomi.
- Mansur Salanke Esq. – Ofishin Sakataren Gwamnati
- Aishatu Abubakar Sadiq – Ma’aikatar Lafiya
- Abdu Na Abdu Ashiru – Ma’aikatar ayyuka
- Shehu Usman Salihu – Hukumar Ma’aikata
- Habib A. Lawal – Ma’aikatar Kudi
- Suwaiba Shehu Ibrahim – Hukumar jin dadin Malamai
- Dr. Mahmud Lawal – ma’aikatar kula da kananan hukumomi
- Linda Asabat Yakubu – ma’aikatar muhalli da ma’adinai
- Ramatu MB Tukur – Hukumar kula da birnin Kaduna
- Mohammed Hayatuddeen – Hukumar kula da birnin Zaria
- Augustine Godwin Alex – Hukumar kula da birnin Kafanchan
- Felicia Indoka Makama – Ofishin Gwamna
- Al-Amin Murtala Dabo – Ofishin Gwamna
Sakatarorin dindindin guda 7 daga cikin tsoffin da aka tabbatar sun hada da:
- Nuhu Isiyaku Buzun – Majalisar zartaswa da Harkokin Siyasa (CPA), Ofishin Sakataren Gwamnati.
- Dr. Haliru Musa Soba – Ma’aikatar Ilimi
- Dr. Yusuf Saleh – Ma’aikatar Kasuwanci, Ƙirƙira da Fasaha
- Abubakar Abba Umar – Ma’aikatar Noma
- Nasiru A. Banki – Ofishin Ma’aikata karkashin ofishin shugaban ma’aikata
- Kabiru M. Mainasibi – Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida
- Bashir Muhammad, mni – Ma’aikatar Tsare-tsare da Kasafin Kudi
Gwamna Sani, ya bukaci sabbi da tsoffin sakatarorin dindindin din da aka nada da su nuna bajintar su cikin himma da gaskiya da adalci.
Gwamnan ya kuma nuna matukar godiyarsa ga daukacin sakatarorin dindindin din da ke barin gado bisa ga gudunmawar da suka bayar ga ci gaban jihar Kaduna, tare da yi musu fatan samun nasara a duk ayyukansu na gaba.