Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya rantsar da sabon Kwamishinan ma’aikatar yada labarai na jihar Malam Ahmed Maiyaki wanda da zai kara taimakawa majalisar Zartarwar Jihar kaimi domin sauke nauyin da Allah ya ɗora masu.
Gwamnan ya rantsar da kwamishinan ne a yayin zaman majalisar Zartarwar jihar wanda ya gudana a dakin taro na fadar gwamnatin jihar a yau Talata 21 ga watan Oktobar 2025.
- Ba A Yi Wa Kiristoci Kisan Gilla A Arewacin Nijeriya – Sarkin Musulmi
- ADC Ta Gargaɗi Gwamnatin Tarayya Kan Amfani da Zargin Juyin Mulki Wajen Yaƙar ‘Yan Adawa
Ahmed Maiyaki wanda shine tsohon Shugaban Hukumar kafafen yada labarai na jihar Kaduna ( KSMC) . Hakazalika, Maiyaki , ya kasance tsohon Daraktan yada labarai na tsohon gwamnan jihar Kaduna Mukhtar Ramalan Yero.
Ahmed maiyaki, ya dade yana bayar da gudummawa a harkar yada labarai a a fadin kasar nan bayan kasancewarsa tsohon ma’aikaci a sashin hausa na rediyon Faransa ( FRI).
Jihar Kaduna ta kwashe shekaru takwas babu ma’aikatar yada labarai wacce tsohon gwamna Nasir El-Rufai ya rufeta , sai bayan lashe zaben gwamna Uba Sani ya dawo da ma’aikatar wacce aka dorawa alhakin kula da yada manufofin gwamnatin jihar .