Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya taya Ambasada Mai Martaba Sarkin Zazzau kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kaduna, Ahmed Nuhu Bamalli murnar bikin cika shekaru 3 da hawansa karagar mulki.
Hakazalika, Gwamna Uba ya mika sakon taya murna ga daukacin masarautun tare da addu’ar Allah ya kara wa Sarkin tsawon rai da nasara akan jagoranci a masarautar.
- An Horas Da Makiyaya Dabarun Shuka Ciyawar Shanu A Kaduna
- Gwamna Uba Sani Ya Bayyana Sabbin Shirye-shiryen Inganta Tsaro A Jihar Kaduna
Mai Martaba Bamalli, a jagorancin masarautar na shekaru uku ya samu gagarumar nasarori a fannin gina kasa, ci gaban al’umma da tabbatar da adalci a zamantakewa. Ya jagoranci tattaunawar sulhu don magance sabani a tsakanin mutane mabanbanta tare da hada kan kabilu da addinatai daban-daban a jihar Kaduna.
“Sarkin, ya jajirce wajen inganta ilimi da kiwon lafiya, musamman a yankunan karkara wanda hakan ya mayar da yara da dama koma wa ajujuwa don samun ilimi da kuma inganta kiwon lafiya.
“Babu wanda zai musanta wadannan muhimman gudummawa da Sarkin ya bayar, hakan ya tabbatar da karamcinsa da nasihars ga kowa da kowa.
“A wannan dan kankanin lokaci, shugabancinsa na hangen nesa alama ce ta ci gaban al’umma, hadin kai, da kyakkyawan fata, wanda ya zama abin koyi acikin al’ummarsa, don haka, ina taya HRH Ambassada, Mai Martaba sarki Ahmed Bamalli murnar zagayowar ranar hawansa karagar mulki, Allah Madaukakin Sarki ya ba shi tsawon kwana, ya ba shi nasara da kuma koshin lafiya.”