Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya gargadi mambobin majalisar zartaswar jihar Kano da su bijirewa duk wani yunkuri da zai iya haifar da rarrabuwar kai a majalisar kwamishinoninsa.
Hakazalika, gwamnan ya tunatar da kwamishinonin al’adun rikon amana Da’a da mutunta juna a majalisar, inda ya sha alwashin daukar matakin hukunta duk wani dan majalisar da ya yi watsi da wannan ka’idoji.
- Ministan Harkokin Wajen Kasar Sin Ya Lashi Takobin Karfafa Hadin Gwiwa Da Afirka
- Kasar Sin Za Ta Hada Hannu Da Kasashen Afirka Wajen Sa Kaimi Ga Zamanintarwa Mara Gurbata Muhalli
Ya bayyana haka ne a yayin bude taron majalisar zartarwar da aka gudanar a zauren majalisar da ke gidan gwamnati, kamar yadda mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya bayyana.
Rahotanni sun bayyana cewa, gwamnan ya yi maraba da sabbin kwamishinoni bakwai da aka nada a majalisar dokokin jihar, inda ya jaddada wajibcin yin riko da gaskiya da kuma cikakken hadin kai.