• English
  • Business News
Saturday, September 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Yusuf Ya Jagoranci Tawagar Kano Zuwa Jana’izar Marigayi Aminu Dantata A Madina

by Sulaiman
3 months ago
in Manyan Labarai
0
Gwamna Yusuf Ya Jagoranci Tawagar Kano Zuwa Jana’izar Marigayi Aminu Dantata A Madina
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya bar filin jirgin sama na Malam Aminu Kano a daren ranar Lahadi yana jagorantar wata tawagar manyan mutane domin halartar jana’izar marigayi hamshakin dan kasuwa kuma dattijon jihar, Alhaji Aminu Alhassan Dantata a birnin Madina na kasar Saudiyya wanda ya rasu da sanyin safiyar Asabar a birnin Abu Dhabi na kasar Dubai.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar.

  • Sojoji Sun Kashe Shugaban Ƴan Ta’adda Mai Dada
  • Sharrin Ƴan Adawa Ne, Gwamnati Ta Ƙaryata Labarin Cire SGF Akume 

Gwamnan yana tare da Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, tare da Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Umar Namadi, tsohon Gwamna Barrista Ali Saad Birnin Kudu da sauran manyan jami’an gwamnati da manyan mutane a jihar.

Labarai Masu Nasaba

Majalisar Shura ta Kano Za Ta Binciki Zargin Batanci Ga Annabi Kan Malam Triumph

’Yansanda Sun Kama ‘Yan Fashi A Kaduna, Sun Ƙwato Bindiga Da Wayoyi

Da yake jawabi jim kadan kafin tashinsa a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, Gwamna Yusuf ya bayyana marigayi Dantata a matsayin uba ga mutane da yawa, wanda karamcinsa da sadaukarwarsa ya wuce iyaka.

Gwamnan ya jaddada cewa, zuwan tawagar a Madina shaida ce ta matukar mutuntawa da jama’a da gwamnatin jihar Kano suke yi masa na gadon alkairai da ya bari kuma a matsayinsa na dattijon jihar.

Ana sa ran jana’izar da za a yi a birnin Madina, za ta samu halartar wakilan jiha da na tarayya, da ‘yan uwa, ‘yan kasuwa, malaman addinin Islama, da masoya daga sassan duniya baki daya, tare da yin addu’ar Allah ya jikansa.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Sojoji Sun Kashe Shugaban Ƴan Ta’adda Mai Dada

Next Post

Murabus Ɗin Ganduje: ‘Yan Kwankwasiyya Na Shirin Ɗaukar Wani Mataki

Related

Majalisar Shura ta Kano Za Ta Binciki Zargin Batanci Ga Annabi Kan Malam Triumph
Manyan Labarai

Majalisar Shura ta Kano Za Ta Binciki Zargin Batanci Ga Annabi Kan Malam Triumph

2 hours ago
’Yansanda Sun Kama ‘Yan Fashi A Kaduna, Sun Ƙwato Bindiga Da Wayoyi
Manyan Labarai

’Yansanda Sun Kama ‘Yan Fashi A Kaduna, Sun Ƙwato Bindiga Da Wayoyi

14 hours ago
NECO 2025: Gwamnan Kano Ya Bayyana Bayanai Ba Daidai Ba
Manyan Labarai

NECO 2025: Gwamnan Kano Ya Bayyana Bayanai Ba Daidai Ba

1 day ago
‘Yancin Kananan Hukumomi: Yadda Gwamnoni Suke Kawo Cikas
Manyan Labarai

‘Yancin Kananan Hukumomi: Yadda Gwamnoni Suke Kawo Cikas

1 day ago
Kwankwaso na Tattaunawa da Shugaban APC Nentawe A Shirye-shiryen Sauya Sheƙa
Manyan Labarai

Kwankwaso na Tattaunawa da Shugaban APC Nentawe A Shirye-shiryen Sauya Sheƙa

1 day ago
Ya Kamata Karancin Malamai A Duniya Ya Zama Darasi Ga Nijeriya
Manyan Labarai

Ya Kamata Karancin Malamai A Duniya Ya Zama Darasi Ga Nijeriya

1 day ago
Next Post
Ganduje Ba Zai Hana Kwankwaso Shiga APC Ba

Murabus Ɗin Ganduje: 'Yan Kwankwasiyya Na Shirin Ɗaukar Wani Mataki

LABARAI MASU NASABA

Majalisar Wakilai Za Ta Sasanta Dangote Da NUPENG

Majalisar Wakilai Za Ta Sasanta Dangote Da NUPENG

September 27, 2025
Yaki Da Miyagun Kwayoyi: Kamfanin LEADERSHIP Da NDLEA Sun Kulla Kawance

NDLEA Ta Farmaki Masu Safarar Muggan Kwayoyi A Sassan Nijeriya

September 27, 2025
Majalisar Shura ta Kano Za Ta Binciki Zargin Batanci Ga Annabi Kan Malam Triumph

Majalisar Shura ta Kano Za Ta Binciki Zargin Batanci Ga Annabi Kan Malam Triumph

September 27, 2025
‘Yansanda Sun Cafke Mutum Hudu Kan Satar Taransifoma A Makaranatar Kebbi

‘Yansanda Sun Cafke Mutum Hudu Kan Satar Taransifoma A Makaranatar Kebbi

September 27, 2025
Tinubu Zai Gana Da Manyan Ƴan Kasuwa, Zai Ƙaddamar Da Muhimman Aiyuka A Legas

Tinubu Zai Gana Da Manyan Ƴan Kasuwa, Zai Ƙaddamar Da Muhimman Aiyuka A Legas

September 27, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Kiwon Kifi

Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Kiwon Kifi

September 27, 2025
Sabon Farashin Jigilar Mahajjata A 2026, Ƴan Arewa N8.2m, Ƴan Kudu N8.5m

Sabon Farashin Jigilar Mahajjata A 2026, Ƴan Arewa N8.2m, Ƴan Kudu N8.5m

September 27, 2025
Dalilin Gwamnatin Tarayya Da Hukumar FAO Na Zuba Dala Biliyan 3.14 A Fannin Noma

Dalilin Gwamnatin Tarayya Da Hukumar FAO Na Zuba Dala Biliyan 3.14 A Fannin Noma

September 27, 2025
Yadda Na Kawo Karshen Yajin Aikin ASUU Cikin Kwana Daya – Jonathan

Lalacewar Tsarin Zabe Babbar Barazana Ce Ga Dorewar Dimokuradiyyar Afirka — Jonathan

September 27, 2025
Ana Fatan Majalisar Wakilan Amurka Za Ta Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Raya Hadin Gwiwar Sin Da Amurka

Ana Fatan Majalisar Wakilan Amurka Za Ta Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Raya Hadin Gwiwar Sin Da Amurka

September 26, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.