Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya umarci masu wurin zama a jerin gidajen Kwankwasiyya City, Amana city, da Bandirawo city da su koma gidajen da zama nan da watanni uku ko kuma a kwace lasisin gidajen su.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Litinin.
- Sin Ta Kaddamar Da Sabon Shiri Kan Tsare-tsaren Musamman Don Bunkasa Sayayya
- Ga Dukkan Alamu Kaikayi Zai Koma Kan Mashekiya
Umarnin ya biyo bayan rantsar da sabon kwamishinan raya birane da gwamnan ya yi a fadar gwamnatin Kano.
“Dole ne mu ci gaba da bunkasa jiharmu, kuma an gina wadannan gidajen ne don habaka jiharmu.
“Ga dukkan masu gidaje da ke wadannan jerin gidaje, ina sanar da su a fili, ko dai su koma wuraren da zama ko kuma a kwace,” in ji Gwamna Yusuf.
Ya kuma bukaci wadanda ba za su iya komawa wuraren ba da su yi tunanin yiwuwar bayar da hayar gidajensu, yana mai jaddada kudirin gwamnati na ganin wuraren sun ci gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp