A ranar Litinin 8 ga Satumba, 2025 ne gwamnatin jihar Kano za ta kaddamar da sabuwar majalisar Shurah, karkashin jagorancin gwamna Abba Kabiru Yusuf. Za a gudanar da bikin kaddamarwar ne a gidan gwamnati dake Kano.
Hakan na kunshe ne acikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar, Ibrahim Abdullahi Waiya ya fitar a 2 ga Satumba, 2025.
- Xi: Alakar Sin Da Rasha Ta Zama Misali Na Kyakkyawar Dangantakar Manyan Kasashe
- Sabuwar Ajandar Kasar Sin Ta Inganta Magance Gibin Kudi A Duniya
Kafa majalisar Shurah na zuwa ne domin karfafa gudanar da mulki cikin hadin kai, da bayyana gaskiya wajen yanke shawara.
Ana sa ran majalisar za ta kasance kamar wata kungiya mai ba da shawara ga Gwamnatin Jihar, domin aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da za su kawo sauyi da kuma bunkasa ci gaba mai dorewa a jihar.
Majalisar Shurah ta kunshi manyan mutane masu kima da daraja sosai, da suka fito daga mazabu daban-daban da nufin tabbatar da daidaito da wadataccen wakilci a dukkan bangarori na zamantakewar al’ummar Kano.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp