Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya bayyana takaicinsa kan yawan tashin hakula da ake samu tsakanin magoya bayan jam’iyyun siyasa a jihar.
BBC ta rawaito cewa, wata sanarwa ta hannun mai taimaka wa gwamnan kan yaɗa labaru, Isa Gusau, ta ce an fi samun rikicin ne tsakanin magoya bayan jam’iyyar APC mai mulki da kuma na PDP mai hamayya.
- Zulum Ya Nemi Afuwar Atiku Kan Harin Da Aka Kai Wa Tawagarsa A Borno
- Zulum Ya Raba Abinci Da Atamfa Na Miliyan 255 Ga Talakawa 70,000
Gwamnan ya buƙaci kwamishinan ƴan sanda na jihar ya gudanar da bincike kan rikice-rikice da aka samu na baya-bayan nan tare da tabbatar da cewa an gurfanar da duk wanda aka samu da laifi.
Ya kuma buƙaci ƴan siyasa da masu ruwa da tsaki, da ƴan takara su tabbatar sun kauce wa rigingimu a lokutan yaƙin neman zaɓe domin kauce wa shiga hannun hukuma.