Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya sauke kwamishinonin biyu daga mukamansu a wani sauyi da ya yi da nufin inganta harkokin gwamnatinsa.
Sauyin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Dauda Iliya, ya fitar ranar Alhamis a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
- Yanzu-yanzu: Sanata Dino Melaye Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP
- Sin Na Ci Gaba Da Kyautata Rayuwar Al’umma Ta Amfani Da Hidimomin Dijital Da Na Kirkirarriyar Basira
Wadanda abin ya shafa sun hada da Kwamishinan Muhalli, Engr. Emet Kois da takwaransa na ma’aikatar harkokin gwamnatoci da ayyuka na musamman, Hon. Tukur Ibrahim Shani.
Gwamna Zulum ya nuna jin dadinsa ga kwamishinonin biyu, tare da yi musu fatan alheri a cikin ayyukansu na gaba.
Sai dai ya sanar da nadin Engr. Mohammed Habib da Ibrahim Hala Hassan domin maye gurbin kwamishinonin biyu da aka sauke.
A halin da ake ciki, Gwamna Zulum ya kuma amince da nadin Farfesa Yusuf Gana Balami a matsayin Shugaban Hukumar Ilimin Sakandare ta Jihar Borno.
Balami, Farfesa a fannin ilimi, ya fito ne daga Hawul da ke kudancin jihar.
Zulum ya taya Balami murna tare da bukatar sa da ya yi amfani da shekarunsa na gogewa a fannin ilimi, a matsayin shugaba a bangaren gudanarwa da karantarwa wajen sake fasalin ilimin sakandare a jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp