Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, a ranar Talata, ya nuna takaicinsa kan sabbin hare-haren Boko Haram inda suka tarwatsa sansanin soji da kuma sace-sacen mutane a kusan kowace rana ba tare da wani hobbasa daga jami’an tsaro ba.
Gwamnan ya ce sabbin hare-haren na nuni da cewa, jihar na samun koma baya a nasarar da aka samu na yaki da ‘yan ta’adda a baya.
- ‘Yansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Satar Mota A Bauchi
- An Buɗe Sabbin Cibiyoyin Kula Da Masu Cutar Sankarau A Jihohi 6
Zulum ya kara da cewa, gwamnatinsa na bayar da goyon baya sosai ga sojoji a yakin da ake yi da ‘yan ta’addan Boko Haram, wanda hakan ya sa aka samu zaman lafiya a cikin shekaru uku da suka gabata.
Sai dai ya koka da yadda hare-haren da aka kai kwanan nan, inda aka tarwatsa sansanonin sojoji a Wajirko, Sabon Gari a karamar hukumar Damboa, Wulgo a Gamboru Ngala, Izge a karamar hukumar Gwoza da sauransu wanda hakan ya yi sanadin kashe mutane ‘yan gari da jami’an tsaro, lallai abun damuwa ne matuka.
Gwamna Zulum ya bayyana haka ne a wani taro na musamman na tsaro wanda ya samu halartar babban kwamandan runduna ta 7 ta rundunar sojojin Nijeriya, Manjo Janar Abubakar Haruna da kwamandojin sassan rundunar da kwamishinan ‘yansanda na jihar da shugabannin sauran hukumomin tsaro.
Taron ya kuma samu halartar Shehun Borno Alh. Dr. Abubakar Garbai Al-Amin El-Kanemi; Shehun Bama, Sarakunan Biu, Uba, Askira, Gwoza, yayin da Shehun Dikwa da Sarkin Shani aka wakilce su.
Zulum ya yabawa gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da jami’an tsaro bisa goyon bayan da suke bayarwa wajen yaki da Boko Haram.
Ya kara da cewa, dole ne a kara kaimi ta hanyar samar da kayan yaki na zamani ga sojoji domin dakile duk wani sabon harin da zai addabi sassan yankin Sahel na Borno da ke kan iyaka da kasashen Jamhuriyar Chadi, Nijar da Kamaru.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp