Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da miƙa ƙudirin doka ga Majalisar Dokokin Jihar domin haramta auran jinsi da kuma wasu aiyukan batsa a jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin taron majalisar zartarwa ta jihar karo na 31 da aka gudanar a ofishin gwamnati na birnin Kwankwasiyya. A wata sanarwa da kakakinsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci tauye darajar addinin Musulunci da al’adun Kano ba.
- ‘Yansanda Sun Cafke ‘Yan Fashi 3 A Kano, Sun Ƙwato Motar Sata
- Akwai Tara Mai Tsauri Ga Duk Wanda Ya Sare Bishiya Ba Bisa Ƙa’ida Ba – Gwamnatin Kano
Ya bayyana cewa ƙudirin ya fi karkata kan hana auran jinsi ɗaya, Madugo da Liwadi, waɗanda ya ce addini da al’ada suka haramta. “Ba za mu taɓa bari wani aiki da ya saɓa wa addininmu da al’adunmu ya samu gindin zama a Kano ba. Wannan gwamnati na da alhakin kare mutuncin tarbiyyar al’ummar mu,” in ji shi.
Idan aka amince da ƙudirin a majalisa, dokar za ta ƙaƙabawa masu aikata ko yaɗa irin waɗannan aiyuka manyan hukunci. Gwamna Yusuf ya nuna ƙwarin gwuiwar cewa ƴan majalisar za su ɗauki matakin gaggawa, tare da bayyana ƙudirin a matsayin muhimmin mataki na kare lafiyar tarbiyya da zamantakewar jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp