Gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno, ya amince da sabon tsarin biyan mafi karancin albashi na Naira 80,000 ga ma’aikatan gwamnatin jihar.
Gwamnan ya kuma kafa kwamitin aiwatarwa domin tabbatar da an fara biyan sabon tsarin albashin cikin sauki tare da shugaban ma’aikatan gwamnatin, Elder Effiong Essien, a matsayin shugaba.
- Tinubu Ya Rushe Wasu Ma’aikatau Tare Da Ƙirƙirar Sabuwa
- Gidauniya Da Gwamnatin Zamfara Sun Tallafa Wa Mata 200 Da Kajin Kiwo
Kwamitin yana da wa’adin wata daya don gabatar da rahotonsa kan daidaita tsarin karin biyan albashin.
Da yake bayyana hakan ga manema labarai a Uyo, a ranar Laraba, Kwamishinan Yada Labarai, Kwamred Ini Ememobong, ya bayyana sauran mambobin kwamitin da suka hada da Shugaban Hukumar Kula da Kananan Hukumomi da Sakatarorin Dindindin a Ma’aikatar Kudi da Ma’aikatar yarjejeniyar ayyukan gwamnati ga huldar jama’a.
Sauran sun hada da Babban Sakatare, Ma’aikatar Kwadago da Tsare-Tsare; Babban Lauyan gwamanti kuma kwamishinan Shari’a; Akanta janar; Babban Sakatare, Hukumar Kula da Ayyukan Gwamnati; Babban Sakatare, Ofishin Shugaban Ma’aikata; Manyan sakatarorin dindindin a ma’aikatar Kasafin Kudi.
Bugu da kari, akwai wakilan kungiyoyi da suka hada da kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC); kungiyar ‘yan kasuwa ta jihar (TUC) da kuma kungiyar ma’aikatan kananan hukumomin Nijeriya (NULGE).