• English
  • Business News
Wednesday, September 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnan Bauchi Ya Aikewa Majalisa Sunayen Kwamishinoni 23 Don Tantancesu

by Sulaiman
2 years ago
in Labarai
0
Gwamnan Bauchi Ya Aikewa Majalisa Sunayen Kwamishinoni 23 Don Tantancesu
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad ya aike wa Majalisa dokokin jihar sunayen mutum ashirin da uku (23) da ya zaba a matsayin Kwamishinoninsa da yake fatan Majalisar za ta tantance tare da amincewa da su a matsayin Kwamishinoni kuma mambobin Majalisar zartaswar jihar. 

Wannan matakin an yi ne bisa dogara da sashin doka kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ta 1999 ta tanadar

  • Gwamnatin Bauchi Ta Ware Rawunan Wasu Hakimai 6 Kan Kutsa Kai Cikin Harkokin Siyasa

A yayin zaman Majalisar na ranar Litinin da kakakin Majalisar, Rt. Hon. Abubakar Y Suleiman ya jagoranta ne Majalisar ta samu sakon gwamnan Bala Muhammad da ke neman a amince da zabin da ya yi wa mutanen a matsayin Kwamishinoni.

Labarai Masu Nasaba

Sowore Ya Maka DSS, Meta da X A Kotu Kan Take Masa Haƙƙi

Saudiyya Ta Saki ‘Yan Nijeriya 3 Da Aka Yi Wa Sharrin Safarar Ƙwayoyi

Shugaban masu rinkaye na Majalisar, Saleh Hodi Jibir ne ya karanta sakon gwamnan.

Kamar yadda yake a jerin sunayen da gwamnan ya aike, karamar hukumar Alkaleri ta samu zababbun Kwamishinoni biyu Maiwada Bello (Geo Barrister) da Ibrahim Gambo; kazalika ita ma karamar hukumar Bauchi ta samu zababbun Kwamishinoni biyu masu suna Mahmoud Babamaji Abubakar da Hon. Danlami Ahmed Kawule; Bogoro: Tsammani Lydia Haruna; Dambam: Ahmed Sarki Jalam; Darazo: Yakubu Ibrahim Hamza; Dass: Usman Santuraki; Ganjuwa: Abdul Hassan; Gamawa: Muhammad Salees; Giade: Dr. Yakubu Adamu.

Saura su ne: Jama’are: Usman Abdulkadir Moddibo; Itas/Gadau: Hajara Jibrin Gidado; Katagum: Hon. Farouk Mustapha; Kirfi: Hajara Yakubu Wanka; Misau: Aminu Hammayo; Ningi: Hassan El-Yakub, SAN; Shira: Muhammad Hamisu Shira; da kuma Tafawa Balewa: Silas Madugu.

Har-ila-yau a karamar hukumar Tafawa Balewa, gwamnan ya zabo Abubakar Abdulhamid Bununu; sannan, ita ma karamar hukumar Toro ta na da zababbun Kwamishinoni biyu Jamila Muhammad Dahiru da Dr. Adamu Umar Sambo; Warji: Abdulrazak Nuhu Zaki, sai kuma a karamar hukumar Zaki, gwamnan ya zabi Amina Muhammad Katagum a matsayin wacce yake so a matsayin Kwamishinoni.

A fadin sanarwar manema labarai da mai magana da yawun kakakin Majalisar, Abdul Ahmad Burra, Hon. Barr. Habibu Umar (Da ke wakiltar mazabar Kirfi) ya bada shawarar Majalisar ta ware ranakun 2, 3 da 4 na watan Augustan 2023 a matsayin ranakun tantance Kwamishinoni. Sai ya samu marawar bayan Hon. Lawan Dauda (Mazabar Sade).

Daga nan Majalisar ta amince da ware ranakun 2, 3 da 4 domin aikin tantance zababbun Kwamishinonin jihar.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Gwamnati Na Aiki Tukuru Don Rage Radadin Tsadar Man Fetur – Akume

Next Post

Mbappe Ya Samu Tayin Fam Miliyan 300 Daga Al Hilal Ta Saudiya

Related

Sowore Ya Maka DSS, Meta da X A Kotu Kan Take Masa Haƙƙi
Manyan Labarai

Sowore Ya Maka DSS, Meta da X A Kotu Kan Take Masa Haƙƙi

2 hours ago
Saudiyya Ta Saki ‘Yan Nijeriya 3 Da Aka Yi Wa Sharrin Safarar Ƙwayoyi
Manyan Labarai

Saudiyya Ta Saki ‘Yan Nijeriya 3 Da Aka Yi Wa Sharrin Safarar Ƙwayoyi

3 hours ago
Sauye-sauyen Manufofin Gwamnati Na Iya Hana Masu HND Zuwa NYSC
Labarai

An Yi Garkuwa Da Wani Mai Hidimar Ƙasa Da Ɗalibi A Jos

12 hours ago
Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Hutun Sati 2 A Ƙasar Faransa
Labarai

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Hutun Sati 2 A Ƙasar Faransa

13 hours ago
Sojoji
Labarai

Sojoji Sun Harbe Wasu ‘Yan Ta’adda 2 A Taraba

14 hours ago
Buhari Ya Taya Amusan Murnar Lashe Zinari A Gasar Tsere Ta Duniya
Labarai

Tinubu Ya Taya Amusan Da Gumel Murnar Samun Nasarori A Ɓangarori Daban-daban

15 hours ago
Next Post
Mbappe Ya Samu Tayin Fam Miliyan 300 Daga Al Hilal Ta Saudiya

Mbappe Ya Samu Tayin Fam Miliyan 300 Daga Al Hilal Ta Saudiya

LABARAI MASU NASABA

Sowore Ya Maka DSS, Meta da X A Kotu Kan Take Masa Haƙƙi

Sowore Ya Maka DSS, Meta da X A Kotu Kan Take Masa Haƙƙi

September 17, 2025
Saudiyya Ta Saki ‘Yan Nijeriya 3 Da Aka Yi Wa Sharrin Safarar Ƙwayoyi

Saudiyya Ta Saki ‘Yan Nijeriya 3 Da Aka Yi Wa Sharrin Safarar Ƙwayoyi

September 17, 2025
Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo

Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo

September 16, 2025
Shawarwarin Sin: Ingantattun Hanyoyi Masu Sauki Na Warware Sabani

Shawarwarin Sin: Ingantattun Hanyoyi Masu Sauki Na Warware Sabani

September 16, 2025
Sauye-sauyen Manufofin Gwamnati Na Iya Hana Masu HND Zuwa NYSC

An Yi Garkuwa Da Wani Mai Hidimar Ƙasa Da Ɗalibi A Jos

September 16, 2025
Sin Da Amurka Sun Yi Tattaunawar Keke-da-keke Kan Batutuwan Cinikayya Da Manhajar TikTok

Sin Da Amurka Sun Yi Tattaunawar Keke-da-keke Kan Batutuwan Cinikayya Da Manhajar TikTok

September 16, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Hutun Sati 2 A Ƙasar Faransa

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Hutun Sati 2 A Ƙasar Faransa

September 16, 2025
Sin Da Ghana Na Fadada Hadin Gwiwa A Bangaren Ciniki Da Zuba Jari

Sin Da Ghana Na Fadada Hadin Gwiwa A Bangaren Ciniki Da Zuba Jari

September 16, 2025
Sojoji

Sojoji Sun Harbe Wasu ‘Yan Ta’adda 2 A Taraba

September 16, 2025
Yawan Hatsin Da Aka Girbe A Kasar Sin Tsakanin Shekarar 2021-2025 Ya Kai Wani Sabon Matsayi

Yawan Hatsin Da Aka Girbe A Kasar Sin Tsakanin Shekarar 2021-2025 Ya Kai Wani Sabon Matsayi

September 16, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.