Shugaban Ma’aikata na Jihar Bauchi, Alhaji Yahuza Adamu Haruna, ya sanar da cewa gwamnatin jihar ta amince da fitar da Naira miliyan 500 domin biyan kudin giratuti cikin hanzari.
Adamu ya bayyana cewa, gwamna Bala Muhammad, ya amince da biyan kudin a yayin zaman majalisar zartaswa na jihar da ya gudana a ranar Juma’a.
Da ya ke magana da ‘yan jarida a ranar Juma’a, Yahuza ya yi bayanin cewa gwamnatin jihar tana aiki tukuru domin biyan dukkanin giratuti da ake bin jihar kara-kataf ta hanyar fito da sabon tsarin biyan kudin fansho a kwanakin baya, wanda tunin gwamnan jihar, Bala Muhammad ya sanya wa tsarin hannu.
“Sanin kowa ne akwai matsaloli da suka dabaibaye wannan gwamnatin da suka mata katutu kan batun biyan basukan giratuti, to amma an dauki matakan da suka dace domin ganin hakan bai ci gaba da faruwa ba, tuni aka samar da mafita kuma aka aiwatar.
“Saboda matsatsin ya yi yawa, kuma gwamna mai jin korafin jama’a ne, don haka ne ya amince da biyan miliyan 500 na giratuti kuma ban take. Ita wannan miliyan 500 na giratuti ne kawai, domin gwamnatin Jihar Bauchi na biyan fansho da albashi yadda ya kamata.”