Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad Abdulkadir, ya amince da bayar da goron Sallah na dubu goma-goma ga dukkanin ma’aikatan gwamnati kama daga na jiha da na kananan hukumomin jihar domin saukaka musu da rage radadin halin da ake ciki.
Kazalika, goron Sallah din an kuma bai wa ma’aikatan ne domin ba su damar gudanar da shagulan bikin Sallah karama cikin walwala da wadata.
- Duk Da Ayyana Nemansa Ruwa A Jallo, Dakta Idris Dutsen Tanshi Ya Dawo Bauchi
- Waɗanda Suka Mutu Yayin Turmutsutsun Karɓar Sadaƙa Ya Ƙaru Zuwa 7 A Jihar Bauchi
A wata sanarwa daga shugaban Ma’aikatan na jihar Bauchi Alhaji Yahuza Adamu Ningi, ya ce domin cigaba da kyautata walwala da jin dadin ma’aikatan jihar ne ya sanya gwamnan amincewa da bada goron Sallar.
Sanarwar mai dauke da sanya hannun babban sakatare Mohammed Sani Umar da ya fitar a ranar Litinin, ya ce, babu shakka goron Sallar za ta taimaka sosai wa ma’aikatan wajen gudanar da shagulan Sallah cikin walwala lura da halin matsin rayuwa da ake ciki a yanzu.
Sanarwar ta nuna irin godiya da jin dadin ma’aikatan bisa wannan kyautar, inda ta kuma yi kira ga ma’aikatan da su ci gaba da mara wa shirye-shiryen gwamnatin Bala Muhammad baya domin kyautata jihar Bauchi a kowani lokaci.
Kazalika, shugaban ma’aikatan ya bukaci dukkanin ma’aikatan jihar da su cigaba da zage damtse wajen yin aiki tukuru domin nausa jihar Bauchi gaba.