Tun bayan da rundunar ‘yansanda ta ayyana neman fitaccen Malamin addinin musuluncin nan, Dakta Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi ruwa a jallo, ba a sake ganin malamin ya bayyana a bainar jama’a ba sai a ranar Litinin 8 ga watan Afrilu, 2024.
Malamin dai ya dawo Bauchi daga hijirar da ya yi tun bayan da tawagar jami’an tsaro suka taba yi wa gidansa kawanya da nufin cafke shi.
- Jami’an Tsaro Sun Yi Dirar Mikiya Gidan Dakta Idris Dutsen Tanshi
- Turmutsitsin Rabon Tallafi Da Zakka: Yadda Mutum 10 Suka Rasu A Bauchi Da Nasarawa
Dakta Idris Abdul’aziz wanda ya samu gagarumin tarba daga magoya bayansa, ana ganin dawowar nasa bai rasa nasaba da kokarin jagorantar Sallah Idi karama da malamin ya saba yi.
Shafin almajiransa wato Dutsen Tanshi Majlisi da ke Facebook ya wallafa bidiyon dawowar malamin na tsawon sama da mintina ashirin tun daga tarbosa har zuwa gidansa da ke Dutsen Tanshi a cikin kwaryar Bauchi.
Idan za a tuna dai a ranar 8 ga watan Fabrairu rundunar ‘yansanda ta shelanta neman malamin ruwa a jallo bisa abun da ta bayyana rashin mutunta umarnin kotu kuma sun samu umarnin kamun ne daga kotu har ma da sanya tukuicin cewa duk wanda ya taimaka mata ta gano inda yake za a ba shi tukuici.
An dai jima ana samun kai ruwa rana da malamin a bisa zargin da ake masa na tada zaune tsaye da yin kalamai na tunzura da ke barazana ga zaman lafiya a jihar Bauchi.
Idan za a tuna dai babban kotun shari’ar Musulumci da ke Bauchi mai lamba ta 1 ta umarci jami’an tsaro da su kamo mata malamin domin domin ya zo gabanta ya ci gaba da fuskantar tuhumar da ake masa na tada zaune tsaye.