Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad, ya mika wa majalisar dokokin jihar daftarin kasafin kudin shekarar badi da yawan su ya kai Naira biliyan N300,219,705,820.60.
Da yake jawabi a zauren majalisar, gwamnan ya ce, an yi hasashen Naira biliyan N178,878,512,477.49 kwatankwacin kaso 59.6 cikin dari zai tafi wajen gudanar da manyan ayyuka, yayin da kuma Naira biliyan N121,341,193,343.11 kwatankwacin kaso 40.4 na kasafin zai tafi wajen gudanar da ayyukan yau da kullum.
- Kwace Wa NNPP Zaben Kano Na Iya Haddasa Tashin Hankali A Afrika – NNPP
- Gwamnatin Kaduna Ta Kaddamar Da Kwamitin Mutum 8 Don Inganta Harkokin Aikin Hajjin 2024
Ya ce, gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen samar da shugabanci na gari.
Ya gode wa majalisar dokokin jihar bisa hadin kai da suke bai wa gwamnatinsa tun a wa’adinsa na farko.
Ya nemi da su kara ba shi hadin kai a wannan lokacin domin dora ayyukan ci gaba a jihar.
A cewarsa, a zamaninsa na farko sun cimma muhimman nasarori, don haka suke fatan cewa a zangonsu na biyu za su kara himma domin kwalliya ta biya kudin sabulu.
A cewar gwamnan an tsara kasafin na 2024 domin bangarorin kiwon lafiya, ilimi, gona, tsaro na daga cikin muhimmanan bangarorin da suka samu kaso mafi tsoka a kasafin badin.
A nasa jawabin, kakakin majalisar dokokin jihar na Bauchi Hon. Babayo Muhammad Akuyam, ya bada tabbacin cewa majalisar za ta nazarci kasafin tare da yin abin da ya dace domin amincewa da kuma ci gaba da gudanar da ayyukan da suka dace a Jihar Bauchi.